EFCC ta tsare madamfaran yanar gizo 4 a Abuja

EFCC ta tsare madamfaran yanar gizo 4 a Abuja

Jami'an reshen kula da masu aikata miyagun laifuka ta yanar gizo na hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC, a ranar Talatar da ta gabata sun samu nasarar cafke wasu 'yan damfara 4 da aka fi sani da Yahoo boys.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, hukumar EFCC ta cafke ababen zargin hudu a wani gida mai lamba 1202 da ke unguwar News Engineering Estate a yankin Dawaki na birnin Abuja.

Rahoton na kunshe a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya gabatar yayin zantawa da manema labarai a ranar Talata, lamarin da ya ce ya biyo bayan wani bincike da leken asiri da aka gudanar a yankin na wani lokaci takaitacce.

Sanarwar babban jami'in hukumar EFCC ta bayyana sunayen 'yan damfaran da suka shiga hannu da suka hadar da Osasu Fred Akioyamem, Ehis Ehizoghie Egheomwan, Chukwuemeka Chanimuya da kuma Oris Karim.

KARANTA KUMA: Tafkin Chadi: Jawaban Buhari a taron Majalisar Dinkin Duniya

A yayin da matasan hudu sun tara dukiya ta hanyar wannan mummunar sana'a, an same su da kayayyaki masu alfarma kuma na more rayuwa kamar motoci, wayoyin salula, na'ura mai kwakwalwa 'yar tafi da gidanka.

Mista Wilson ya kara da cewa, za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban Kuliya da zarar bincike ya kammala.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel