Ba mu son motocinka, ka rike abinka – Yan majalisun dokoki ga Gwamna Obiano

Ba mu son motocinka, ka rike abinka – Yan majalisun dokoki ga Gwamna Obiano

Gaskiya ne ba duka aka taru aka zama daya ba, yayin da ake kuka da wasu yan majalisun saboda sun zama tamkar yan amshin shata ga gwamnonin jahohinsu, su kuwa yan majalisun dokokin jahar Anambra sun fita Zakkah.

Jaridar The Nation ta ruwaito yan majalisar dokokin jahar Anambra sun yi fatali da tayin wasu motocin alfarma guda 30 da gwamnan jahar, Willie Obiano ya yi musu, wanda duk daya ta kai kimanin naira miliyan 30, a jimlace kusan naira biliyan 1 kenan.

KU KARANTA: Mabiya darikar Kwankwasiyya sun yi ma Pantami ihun ‘Ba ma yi’, Kwankwaso ya yi shiru

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan majalisun sun bayyana dalilinsu na yin watsi da tayin da gwamnan ya yi musu, inda suka ce barnar kudi kawai yake ji, inda suka ce idan da gaske yake zai saya musu motoci me yasa ba zai saya a wajen kamfanin gida na Innoson ba?

Wannan tayi na Gwamna Obiano ya biyo bayan korafin da wasu yan majalisa suka yi game da kudaden alawus alawus dinsu da kuma sauran hakkokinsu da suka ce basa zuwa a kan lokaci, don haka gwamnan ya yanke shawarar sayo musu motoci domin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Sai dai yan majalisun sun ce be zasu amshi Toyota Prado SUV da gwamnan ke kwadayin sayo musu a kan naira biliya daya ba saboda almubazzaranci ne, musamman yadda za’a iya samun motocin a kan kudi kalilan daga kamfanin Innoson dake jahar ta Anambra.

Yan majalisun sun kara da cewa dukkanin gwamnonin jahohin kudu maso gabashin Najeriya suna sayen motoci daga hannun kamfanin Innoson, amma banda Obiano, wanda yak e kiyayya da kamfanin dake kera motoci a jaharsa.

Sai dai kaakakin gwamnan, Emma Madu ya karyata rahoton sayen ma yan majalisun motoci, inda yace fadar gwamnatin jahar bata da wata masaniya game da wani shiri da Gwamna Obiano ke yi na saya ma yan majalisun dokokin jahar motoci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel