Masu kokawa kan yawan bashi, "'Yan mu na Masana ne" da ba su taba tabuka komai ba - Fashola

Masu kokawa kan yawan bashi, "'Yan mu na Masana ne" da ba su taba tabuka komai ba - Fashola

Ministan ayyuka da gidaje a Najeriya, Raji Babatunde Fashola, ya dura kan masu fitowa su na yin Allah-wadai da yawan bashin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ke ci daga bankunan Duniya.

Raji Babatunde Fashola SAN, yake cewa masu yawan sukar gwamnati a kan haka bara-gurbin masana tattali ne wanda sam ba su da cikakken ilmin yadda sha’anin tattalin arziki ya ke tafiya.

A wani jawabi da Ministan ya yi a Makarantar koyar da harkar tattalin arzikin nan da ke Legas, ya tattauna a kan yadda tsare-tsaren gwamnati ke da tasiri kan jama’a da kuma cigaban al’umma.

A nan ne Ministan yake nunawa ‘yan jarida cewa mafi yawan masu suka game da karbo aron kudin da gwamnatin kasar nan ta ke yi, mutane ne wanda ba su samu wata nasara a rayuwa ba.

Minista Raji Fashola ya kira su da ‘yan koma-bayan masanan tattalin arziki inda ya kare gwamnati da cewa yanzu babu wata jihar Najeriya da gwamnatin tarayya ba ta aikin hanyoyi.

KU KARANTA: Mu na yaki da cin hanci da rashawa babu daga kafa - Buhari

Fashola ya yi dai-daya da masu kukan cin bashin da cewa: “Wasu ‘Masana’ da ba su taba nunawa Duniya za su iya rike ko da karamin kasuwanci ba, su ne ke ihu don gwamnati ta ci bashi.”

Tsohon gwamnan ya ke cewa ana karbo wannan bashi ne a batar domin a gina abubuwan more rayuwa. Ministan ya bada misali wanda ake tunani da Aliko Dangote ya ke nufi, inda ya ke cewa:

Wani ya karbi aron Biliyoyin Daloli domin ya gina matatar mai, da kamfanin samar da takin zamani, da gas da sauransu, amma wasu ‘yan mu-na masana su na kukan Najeriya za ta ci bashi.”

Mista Fashola ya kara da: “Ana kukan Najeriya da ke da daruruwan miliyoyin jama’a ta ci bashi domin ta gyara hanyoyin dogo na jirgin kasa, da tashohin ruwa da filin jirgi da tituna, da wuta.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel