Ba za mu sanya baki a rigimar Osinbajo da fadar shugaban kasa ba – Majalisar dattawa

Ba za mu sanya baki a rigimar Osinbajo da fadar shugaban kasa ba – Majalisar dattawa

Majalisar dattawa ba za ta saya baki a zargin rigimar da ke fadar Shugaban kasa ba, inji kakakin majalisar, Sanata Adedayo Adeyeye.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Adeyeye ya fadi hakan ne a yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai bayan zaman majalisa a Abuja a ranar Talata, 24 ga watan Satumba.

Adeyeye yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari na da damar sa hadumansa aiki, inda yace baida masaniyar cewa an janye wani aiki da yake na mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ne.

Yace: “Majalisar dattawa bata da alaka da wannan sannan bamu damu da abunda ya faru da bangaren zartarwa ko abubuwan da ke faruwa da bangaren ba.

“Ina Magana ne da yawun majalisar dattawa. Bana cima bangaren zartarwa albasa sannan kuma bana son damun kaina da abunda ya shafi mataimakin Shugaban kasa ko bangaren zartarwa. Ba matsalarmu bane.

“Wannan matsalar bangaren zartarwa ne kuma mu bama sanya masu baki. Me zai sa muyi haka?”

KU KARANTA KUMA: Keyamo yayi martani yayinda Buhari ya mayar dashi ma’aikatar kwadago

A wani labari kuma, Legit.ng ta rahoto cewa majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata 24 ga Satumba ta nemi Ministan lamurran ‘Yan sanda Maigari Dingyadi da kuma na harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola da su bayyana a gabanta.

Kari a kan wadannan mutum biyu, majalisar ta kira Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu a kan sanin musabbabin tabarbarewar tsaro a Najeriya da kuma isalin Kwalejin ‘yan sanda wadda ke karamar hukumar Tai cikin jihar Ribas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel