Keyamo yayi martani yayinda Buhari ya mayar dashi ma’aikatar kwadago

Keyamo yayi martani yayinda Buhari ya mayar dashi ma’aikatar kwadago

Festus Keyamo (SAN) yayi martani akan sauya masa wajen aiki daga ma’aikatar harkokin Niger Delta zuwa ma’aikatar kwadago da daukar ma’aikata.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara nada Keyamo a matsayin karamin ministan harkokin Niger Delta kafin ya sauya masa wajen aiki.

Sai dai kuma, an umurce shi da ya sauya matsayinsa tare da na karamin ministan kwadago, Tayo Alasoadura, wanda a yanzu aka mayar da shi ma’aikatar harkokin Niger Delta.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi daga daraktan labarai a ofishin babban saataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey.

Da yake martani akan lamarin, Keyamo ya wallafa a shafin twitter a ranar Talata, 24 ga watan Satumba, cewa a shirye yake yayi aiki a ko ina a gwamnatin Buhari.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Wata daya bayan nada ministoci, Buhari yayi sauye-sauye cikin Ministocinsa

“Akan tafiyar kuma: Aiki biyu cikin watanni biyu! Yanzun nan aka mayar dani ma’aikatar kwadago da daukar ma’aikata domin aiki tare da dan uwana na dogon lokaci, mai girma Chris Ngige. Nagode ya Shugaban kasa da ka ga cancanta na shawagi. A kullun a shirye nake nayi aiki a ko ina,” inji Keyamo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel