Buhari ga shuwagabannin duniya: Muna yaki da rashawa ba sani ba sabo

Buhari ga shuwagabannin duniya: Muna yaki da rashawa ba sani ba sabo

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana ma shuwagabannin kasashen duniya cewa yana yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya babu sani babu sabo, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron majalisar dinkin duniya da yake gudana a birnin New York na kasar Amurka, a ranar Talata, 24 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Gwamnan Borno zai baiwa mutane miliyan 2 marasa aikin yi aiki

Buhari ne shugaban kasa na 5 daya gabatar da jawabi a yayn taron, inda yace: “Shari’ar da muke yi da kamfanin P&ID a kokarinsu na damfarar Najeriya biliyoyin daloli, muna yi ne don sanar da miyagun kungiyoyi ne cewa mu ba kanwar lasa bane.

“Muna kira ga kamfanonin kafafen sadarwa dasu dauki mataki a kan masu kashe tayar da rikici ta hanyar kafafen sadarwa, bai kamata a kyale mutane suna yin yadda suka ga dama ba, saboda irin haka ne ke haddasa tashin tashina dake kai ga asarar rayuka.” Inji shi.

Shugaba Buhari yace babbar matsala ita ce talauci, saboda shi ne ke haddasa duk wani nau’I na miyagun ayyuka tun daga ta’addanci, fasa kauri, safarar mutane da kuma matsalolin da hakan ke janyowa.

“Don haka akwai bukatar yaki da rashawa domin cimma cigaban muradun karni. A zaben 2019, yan Najeriya sun nuna ma duniya cewa basa tare da siyasar batanci, sun rungumi siyasar zaman lafiya.” Inji shi.

A wani labarin kuma, shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya sauya ma wasu ministoci guda biyu ma’aikatu, inda ya tura Festus Keyamo karamin ministan kwadago, inda ya mayar da Alasoudara karamin ministan Neja Delta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel