Zargin safarar kwaya: Jerin sunayen 'yan Najeriya 23 da kasar Saudiyya ta zaratar wa haddi

Zargin safarar kwaya: Jerin sunayen 'yan Najeriya 23 da kasar Saudiyya ta zaratar wa haddi

Jaridar The Nation ta wallafa wani rahoto da ke cewa kasar Saudiyya ta zartar da hukucin kisa a kan wasu 'yan Najeriya 25 bisa zarginsu da laifin safarar kwayoyi zuwa kasar.

A cikin shekarar nan ne kasar Saudiyya ta sako wasu 'yan Najeriya biyu daga cikin wadanda ta tura gidan yari kafin a zartar musu da hukunci, gwamnatin kasar Saudiyya ta sako mutanen ne bayan gwamnatin Najeriya ta shiga lamarin.

Ga jerin sunayen mutanen da jaridar ta wallafa cewa a n yanke wa hukuncin kisa a kasar Saudiyya.

Zargin safarar kwaya: Jerin sunayen 'yan Najeriya 25 da kasar Saudiyya ta zaratar wa haddi
Jerin sunayen 'yan Najeriya 25 da kasar Saudiyya ta zaratar wa haddi
Asali: Twitter

Ko a shekarar da ta gabata sai da Legit.ng ta wallafa wani labari a kan wasu 'yan Najeriya su 14 da aka tura kurkuku a Madinah ta kasar Saudiyya sun aiko wa shugaba Buhari sakon neman taimako domin ya kubutar da su daga wukar hauni.

DUBA WANNAN: Daukaka kara: Alkalai 7 da zasu saurari karar Atiku a kotun koli

Ana tuhumar 'yan Najeriyan ne da tu'ammali da miyagun kwayoyi a kasar Saudiyya, kuma kasar tana zartar da hukuncin kisa ne ga duk wadanda suka aikata irin wannan laifi.

Saidai 'yan Najeriyar sun tsorata bayan an tura su gidan yari, suna masu cewar basu aikata laifin ba kuma kasar ba zata yi masu adalci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel