UNGA: Najeriya ba za ta ba duniya kunya ba – Buhari

UNGA: Najeriya ba za ta ba duniya kunya ba – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaidawa taron Majalisar dinkin duniya cewa zaben Tijjani Muhammad Bande a matsayin shugaban majalisar a zagaye na 74 ba zaben tumun dare bane.

Buhari ya ce Najeriya ba zata ba wa duniya kunya ba, saboda zaben Bande abu ne wanda ya farantawa dukkanin ‘yan Najeriya rai, inji Shugaban kasan.

KU KARANTA:Mutum 2 sun samu rauni a sakamakon harin da ‘yan fashi suka kai dakin kwanan daliban Jami’ar IBB Lapai

Bugu da kari ya sake cewa, nauyin da ya rataya a wuyan Najeriya ba abin wasa bane saboda haka kasashen duniya su kwantar da hankalinsu kasancewar komi zai tafi daidai.

Da yake magana game da sabon Shugaban majalisar dinkin duniyan wato Muhammadu Bande, Shugaban kasan ya ce: “Ambasada Muhammad Bande jakada ne nagari, kuma ko shakka babu na san da irin kwarewarsa zai bai wa mara dan kunya bisa wannan nauyi da aka daura masa.”

Idan baku manta ba majiyar Legit,ng ta kawo maku labarin cewa a yayin da Shugaba Buhari ya isa birnin New York ranar Litinin 23 ga Satumba ya ziyarci sabon shugaban majalisar dinkin duniya Farfesa Tijjani Bande.

A wannan gabar ne ma mai magana da yawun bakin Buhari, Femi Adesina ya ce shugaban kasan ya shawarci Bande da ya san cewa nauyi ne yanzu ya rataya a wuyansa, kuma ka day a manta cewa ilahirin ‘yan Najeriya su na tare da shi.

Ga kadan daga cikin kalaman Buhari wanda wakilinmu ya samu damar kawo maku: “Ina matukar tayaka farin ciki da lashe wannan zabe. Dukkanin kasashen duniya sun yi na’am da zabenka.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel