Yanzu-yanzu: Gwamna Umahi ya kori babban sakaren yada labaransa

Yanzu-yanzu: Gwamna Umahi ya kori babban sakaren yada labaransa

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya sallami babban sakataren yada labaransa, Mista Emma Uzor kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A wani sako da gwamnan ya fitar a ranar Talata, ya ce ya sallami Mr Uzor ne saboda samunsa da bayar da wasu bayyanai da suka saba da ra'ayinsa da na sauran gwamnonin yankin Kudu maso gabas.

A sakon da ya wallafa, Umahi ya ce, "Na bayar da umurnin sallamar babban sakataren yada labarai na saboda samunsa da fadin wani sako da ya saba da ra'ayina a kan shirin kiwo na kasa a madadi na bayan taron NEC da muka yi na baya-bayan nan.

"Ban bawa tsohon sakataren yada labaran izinin magana a kan batun ba.

"Ra'ayinsa ya banbanta da nawa da kuma na sauran gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas.

DUBA WANNAN: Yadda yarjejeniya da aka kulla tsakanin tsohon gwamnan PDP da Buhari kafin zabe ta samu tangarda

"Sanarwar tasa abin kunya ne a gare mu. Zai mika aiki ga sakataren na (Clement Nweke) nan take sannan muna masa fatan alheri."

Sakataren gwamnatin jihar Dr Kenneth Ugbala ya kuma sanar da korar tsohon sakataren yada labaran a gidan rediyon jihar Ebonyi.

Yayin sanarwar, ya ce dalilin korar tsohon sakataren yada labaran ya shafi batun tsaron kasa inda ya bayyana cewa lamarin abin kunya ne ga Umahi da sauran gwamnonin yankin ne Kudu maso Gabas.

Korar Uzor yana zuwa ne wata guda bayan korar tsohon kwamishinan sadarwar da wayar da kan al'umma na jihar, Ken Ohuo a kan dalilin rashin nuna kwazo wurin aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel