Rashin Imani: Yan bindiga sun amshe N250,000 sun kashe wanda suka sata a Kaduna

Rashin Imani: Yan bindiga sun amshe N250,000 sun kashe wanda suka sata a Kaduna

Iyalan wata mata mai suna Esther Katung sun bayyana damuwarsu bisa cin amanar da masu garkuwa da mutane suka nuna musu, bayan sun sace Esther, har ma sun kasheta, sa’annan suka amshi kudin fansa naira 250,000.

Jaridar The Cables ta ruwaito a ranar 14 ga watan Satumba ne yan bindigan suka yi awon gaba da Esther a gidanta dake a kauyen Bagoma dake cikin karamar hukumar Birnin Gwari na jahar Kaduna, sai dai mijinta, Ishaku Katung ya tsere yayin da yan bindigan suka far musu.

KU KARANTA: Ta Allah ta yi: Cutar shawara ta halaka wani gagararren mai garkuwa da mutane a Zamfara

Wani dan uwar matar ya bayyana cewa Esther tare da wasu mutane biyu sun tsere daga hannun yan bindigan a cikin, amma yan bindiga suka bi sawu, inda suka ci karo da Esther, suka sake kamata, nan take suka karya mata kafa, suka kuma tarwatsa mata kai, nan take ta mutu.

Daga nan sai suka jefar da gawarta a cikin dajin, amma basu shaida ma iyalanta ba, suka matsa a kan lallai sai an biyasu kudin fansa naira miliyan 5 kafin su saketa, amma daga bisani suka yarda a kan N250,000.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito su kansu wadanda suka tafi kai kudin fansar da kyar suka sha, sakamakon yan bindigan sun kona baburansu bayan sun amshe kudi, sai bayan kwana biyu aka tsinci gawar Esther ya fara rubewa.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, reshen jahar Kaduna, Joseph Hayab ya bayyana cewa ran mutum ya zama mara daraja a Najeriya, inda yace lamarin ya tsoratasu, kuma a cikin tashin hankali suke zama.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin kaakakin Yansandan jahar Kaduna, DSP Yakubu Sabo domin jin ta bakinsa game da lamarin ya ci tura ssakamakon wayoyinsu a kashe suke.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel