Yadda wata mata ta lakadawa surukarta duka har sai da ta suma

Yadda wata mata ta lakadawa surukarta duka har sai da ta suma

A ranar Talata 24 ga watan Satumba ne aka gurfanar da wata mace mai shekaru 30 da haihuwa, Adenike a gaban kotun Majistare da ke Ado-Ekiti da aka ce ta lakadawa surukarta duka har sai da ta suma.

The Punch ta ruwaito cewa ana tuhumar Adenike da laifin yunkurin aikata kisar gilla.

Dan sanda mai shigar da kara, Sufeta Bankole Olasunkanmi ya shaidawa kotu cewa wanda aka yi karar ta aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Satumba a garin Ado Ekiti.

Olasunkanmi ya ce wanda aka yi karar ta kaiwa surukurta mai shekaru 63, Mrs Comfort hari.

Ya ce wacce aka kai wa harin har yanzu tana sume ba ta farfado ba.

DUBA WANNAN: Yadda yarjejeniya da aka kulla tsakanin tsohon gwamnan PDP da Buhari kafin zabe ta samu tangarda

Olasunkanmi ya ce laifin ya ci karo da sashi na 320 da dokar masu aikata laifi ne 2012 na jihar Ekiti.

Ya bukaci kotun ta bayar da umurnin ajiye wanda akayi karar a gidan gyaran hali kafin lokacin da za a samu shawara daga ofishin direktan tuhume-tuhume na jihar.

Kotun ba ta saurari bangaren wacce aka yi kara ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa aThe lkalin kotun, Mista Abdulhamin Lawal ya bayar da umurnin cigaba da ajiye wacce aka yi karar a gidan gyaran hali ya kuma dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 17 ga watan Oktoban 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel