Ganduje ya yi wa Saudiyya jinjina ta musamman don gudunmawa da ta ke bawa Kano a fanin Ilmii

Ganduje ya yi wa Saudiyya jinjina ta musamman don gudunmawa da ta ke bawa Kano a fanin Ilmii

Gwamnantin Jihar Kano ta yabawa kasar Saudiyya kan irin muhimmiyar gudunmawa da ta bawa jihar a bangaren cigaba da inganta ilimi.

Wannan jawabin na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yadda labarai na mataimakin gwamnan jihar, Hassan Fagge da ya rabarwa manema labarai a Kano.

Musa Fagge ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya jinjinawa kasar Saudiyya ne yayin bikin ranar kasar Saudiyya karo na 89 da ofishin jakadancin Saudiyya da ke Kano ya shirya.

Ya ce mataimakin gwamnan, Alhaji Nasiru Gawuna ne ya wakilci Ganduje a wurin bikin.

Ya mika godiyarsa kan tallafin da Saudiyya ke bawa 'yan Kano domin zuwa jami'o'in kasa mai tsarkin suyi karatu.

DUBA WANNAN: Yadda yarjejeniya da aka kulla tsakanin tsohon gwamnan PDP da Buhari kafin zabe ta samu tangarda

"Kusan shekaru 50 da suka gabata, daliban ilimi daga jihar Kano sun tafi Saudiya don zurfafa karatun addinin wanda hakan ya basu damar koyar da ilimin addini na ainihi ga al'umma tare da taimakawa wurin samar da zaman lafiya a jihar.

"A baya-bayan nan, tallafin da jakadar Saudiyya ya bamu yayin kaddamar da shirin ilimi kyauta kuma wajabi ga dukkan 'yan jihar alheri ne da mutanen Kano za su dade ba su manta da shi ba," inji shi.

Ganduje ya ce kasar Saudiyya tana da muhimmanci a tarihin duniya da kuma zukatan biliyoyin al'umma a duniya.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa kasar Saudiyya ta ware ranar 23 ga watan Satumba domin murnar ranar kasar a dukkan duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel