Kwankwasiyya: Kashi na farko na daliban Kwankwasiyya zasu daga zuwa kasashen ketare karo karatu

Kwankwasiyya: Kashi na farko na daliban Kwankwasiyya zasu daga zuwa kasashen ketare karo karatu

- Kashin farko na dalibai 370 daga jihar Kano na wadanda suka kammala digirin farko zasu daga zuwa kasashen ketare karo karatu

- Kungiyar Kwankwasiyya ta jihar karkashin shugabancin tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso ce ta dau nauyinsu

- Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin dasawa daga inda Kwankwaso ya tsaya a fannin habbaka ilimin daliban jihar

Kashin farko na dalibai 370 daga jihar Kano na wadanda suka kammala karatun jami'a da digiri mai darajar farko zasu wuce kasashen Sudan da India don yin digiri na biyu.

Kungiyar cigaba ta kwankwasiyya wacce Madugu tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ce ta dau nauyinsu.

Jaridar Daily Nigerian ta bada rahoton cewa, daliban sun fito ne daga kananan hukumomi 44 na jihar inda aka samar musu da gurbin karatu a jami'o'i 3 na kasar India da jami'a daya ta kasar Sudan.

A yayin da yake jawabi ga wadanda zasu mori wannan damar a gidansa da ke Kano a ranar Talata, tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso ya ce dalibai 234 zasu yi digiri na biyu ne a fannin kimiyya da fasaha a kasar India, 8 daga ciki zasu yi digirinsu na biyu ne a fannin ilimin addinin musulunci da yaren larabci a kasar Sudan.

Kwankwaso ya bayyana cewa kungiyar ta biya dukkan kudin makarantar daliban wanda ya hada da na makaranta, wajen zama, abinci da kuma inshorar jami'o'in.

KU KARANTA: Tirkashi: Ya kashe kansa akan ya fadi wasan Bet9ja

Kamar yadda ya ce, tuni aka samarwa da daliban tikitin jirgin dawowa gida bayan sun kammala karatunsu.

"Yau ranar tunawa ce gareni, ranar da zamu ga wucewar kashin farko na dalibai 370 da kungiyar Kwankwasiyya ta dau nauyin karatunsu a kasashen ketare. Ilimi shi ne jigon Kwankwasiyya saboda shi ne gishirin zaman duniya."

"Mun yi wa ilimi bauta mai yawa lokacin da muke shugabanci a jihar Kano. Yanzu kuma mun ga yakamata ne mu cigaba," in ji Kwankwaso.

Kwankwaso, tsohon sanata ne a majalisar Najeriya ta 8, ya bukaci daliban da su zama jakadai na gari yayin zamansu a kasashen biyu tare da tabbatar musu da cewa shirye-shiryen dalibai kashi na biyu na nan tafe.

Dan takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP, Abba Kabiru Yusuf ya taya daliban da zasu tafi karatun murna.

Yusuf ya yi alkawarin cigaba da daukar nauyin dalibai matukar ya yi nasara a kotun kuma ya zama gwamnan jihar.

Ya kara da cewa tunanin Kwankwasiyya duk na cigaban Dan Adam ne.

Yusuf ya yi alkawarin farfado da cibiyoyi 26 da gwamnatin Kwankwasiyya ta kirkiro wacce ake zargin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da watangarar da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel