Mutum 2 sun samu rauni a sakamakon harin da ‘yan fashi suka kai dakin kwanan daliban Jami’ar IBB Lapai

Mutum 2 sun samu rauni a sakamakon harin da ‘yan fashi suka kai dakin kwanan daliban Jami’ar IBB Lapai

Wani aikin ‘yan fashi da makami ya bar dalibai biyu da muggan raunuka a lokacin da ‘yan fashin suka far masu a wani dankin kwanan daliban Jami’ar IBB Lapai dake wajen jami’ar.

Wannan aika-aikar na zuwa ne kimanin makonni uku da wani abu makamancinsa ya auku a daya daga cikin dakunan kwanan daliban Jami’ar ta IBB Lapai.

KU KARANTA:Gwamna Badaru ya kaiwa Majalisar Jigawa sunayen kwamishinoni guda 11

Fashi da makami da ya faru daga bayan nan, ya auku ne a dakin kwanan daliban da ake yiwa lakani da ‘Jagaba Lodge’ da misalin karfe 1:00 daren ranar Litinin.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ‘yan fashin sun karbewa daliban kudinsu, wayoyinsu na hannu, na’ura mai amfani da kwakwalwa da kuma sarkoki da ‘yan kunne.

Daya daga cikin daliban da wannan iftila’i ya rutsa da su, Abdulhadi Danyaya wanda ke shekara ta farko a fanni karatun Kimiyyar na’aura mai amfani da kwakwalwa ya samu mummunan rauni a kansa sakamakon sarar adda.

A cewar wani ganau wanda lamarin ya auku a bisa kan idonsa, ya shaida mana cewa Abdulhadi ya samu damar burma wa daya daga cikin ‘yan fashin wuka a cikinsa.

Haka zalika wani ganau ya sake sanar da mu cewa: “Tabbas daya daga cikin daliban ya dabawa daya cikin ‘yan fashin wuka a ciki, hakan ne ma ya sanya suka yi gaggawar barin wurin.”

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da aukuwar wannan lamari tab akin kakakinta, DSP Muhammad Abubakar,

Ya tabbatar mana da cewa mutane biyu ne suka samu rauni, kuma an samu nasarar damke mutum bakwai daga cikin wadanda ake zargi da aikata wannan laifi.

https://thenationonlineng.net/two-students-injured-as-robbers-attack-ibbu-lapai-hostel/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel