Cutar zazzabin Lassa ta hallaka mutum daya a jihar Benue

Cutar zazzabin Lassa ta hallaka mutum daya a jihar Benue

- Kwamishinan lafiya na jihar Benue ya bayyana cewa cutar zazzabin Lassa ta hallaka mutum daya a jihar

- Tuni dai an tura jami'an lafiya yankin don ziyarta tare da tabbatar da cewa cutar bata cigaba da yaduwa

- An samu barkewar cutar a jihohin Nasarawa, Taraba da Filato a cikin jihohin arewacin kasar nan

Kwamishinan lafiya na jihar Benue, Dr Sunday Onbabo, ya tabbatar da mutuwar mutum daya a jihar sakamakon zazzabin Lassa.

Ongbabo ya bayyana hakan ne a takardar da ya mika ga manema labarai a Makurdi babban birnin jihar.

"Jihar Benue ta fuskanci mutuwar mutum daya a ranar 14 ga watan Satumba, 2019. Jam'an hadin guiwa tuni suka ziyarci wajen don gujewa yaduwar cutar," ya sanar.

KU KARANTA: Tirkashi: Ya kashe kansa akan ya fadi wasan Bet9ja

Kwamishinan ya kara da cewa, "Ana sanar da mutane cewa an samu barkewar cutar zazzabin Lassa a makwaftan jihohi kamar Nasarawa, Taraba da Filato a cikin jihohi 19 na arewacin kasar nan daga watan Augusta, 2019 zuwa yau. An samu mutane 60 da cutar inda 16 suka rasa ransu a fadin kasar nan."

Ta takardar, Ongbabo ya shawarci jama'a da su kiyaye hanyoyin samun cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel