To fah: Sai sun nemi suyi zina dani kafin su sanya ni a fim - Jaruma ta tonawa masu shirya fina-finai asiri

To fah: Sai sun nemi suyi zina dani kafin su sanya ni a fim - Jaruma ta tonawa masu shirya fina-finai asiri

- Wata jarumar fim ta kudancin Najeriya ta bayyana wani sirri da yake a boye a masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood

- Ta bayyana cewa yawancin masu shirya fina-finai na kamfanin Nollywood sai sun nemi su kwanta da ita kafin su sanyata a fim

- Ta ce kusan dalilin da ya sanya ba ta fitowa a fim sosai kenan, kuma ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara bayyana sunayensu

Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood Chesan Nze ta fito ta fede biri har wutsiya, inda ta bayyana yadda masu shirya fina-finai na Nollywood suke cewa sai sun kwanta da jarumai mata kafin su saka su a fim.

A bayyanin da ta wallafa, jarumar ta bayyana abinda yasa kwanan nan ba a ganinta a fim sosai.

Jarumar ta bayyana cewa yawancin masu shirya fina-finai ma'ana 'Producers' suna nuna kwadayinsu karara akan jarumai mata wajen neman yin zina da su kafin su basu dama su fito a fim.

KU KARANTA: Hotuna: Yadda wani mutumi ya shiga gida ya iske matar shi kwance da wani kato a kan gadonsu na Sunnah

Jarumar wacce ta nuna bacin ranta akan abinda masu shirya fina-finan suke yi, ta bayyana cewa yanzu baza ta fadi sunan kowa a cikinsu ba, amma kuma idan har aka kai ta makura zata fito ta bayyana uban kowa ma ya sani.

Ana ta faman samun maganganu da suke nuni da cewa akwai badala da ake aikatawa a wajen shirya fina-finai musamman na kudancin Najeriya wato Nollywood, to sai dai kuma hatta na arewacin Najeriyar suma ba su tsira ba, domin kuwa ana ganin suma sun dauki sawun 'yan kudancin Najeriyan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel