Toh fa: Rundunar soji ta kama wasu daliban jam'ia da ke basaja a matsayin 'yan Boko Haram

Toh fa: Rundunar soji ta kama wasu daliban jam'ia da ke basaja a matsayin 'yan Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya a jihar Borno ta kama wasu dalibai maza da ke karatu a jami'ar Maiduguri bisa zarginsu da yin basaja a matsayin mambobin kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram domin yi wa 'yan uwansu dalibai sata da kwace.

A wani faifan bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta, an ga dakarun soji tare da daliban da suka kama.

A cikin faifan bidiyon, wani babban jami'in rundunar soji ya shaida wa manema labarai da ke wurin cewa daliban na yin sojan gona a matsayin mambobin kungiyar Boko Haram.

"Dukkansu na ikirarin cewa su mambobin kungiyar Boko Haram ne. Mu na zargin cewa ba lallai ne mambobin kungiyar Boko Haram ne suka kai harin baya bayan nan da aka kai cikin jami'ar Maiduguri ba. Watakila irin wadannan daliban ne suka kai harin domin su samu damar yin sata.

"Ba lallai mambobin kungiyar Boko Haram ba ne, amma suna fake wa da tsoron mambobin kungiyar da ake yi domin aikata miyagun laifuka," a cewar babban sojan.

DUBA WANNAN: Daukaka kara: Alkalai 7 da zasu saurari karar Atiku a kotun koli

A ranar 15 ga watan Satumba ne dakarun rundunar soji suka dakile wani hari da ake kyautata zaton mambobin kungiyar Boko Haram ne suka kai.

A jawabin da ya gabatar a faifan bidiyon, babban sojan ya ce daliban jami'ar na amfani da sunan kungiyar Boko Haram domin aikata miyagun laifuka.

Toh fa: Rundunar soji ta kama wasu daliban jam'ia da ke basaja a matsayin 'yan Boko Haram
Rundunar soji ta kama wasu daliban jam'ia da ke basaja a matsayin 'yan Boko Haram
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel