EFCC bata zabe a yaki da take yi da rashawa - Magu

EFCC bata zabe a yaki da take yi da rashawa - Magu

Mukaddashin Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu yace hukumar bata nuna wariya wajen yaki da rashawa da take yi a kasar.

Yayi bayanin cewa mafi akasarin mutanen da ke zargin hukumar da bangaranci a yaki da rashawa sun kasance mutane mafi aikata rashawa a kasar.

Mukaddashin Shugaban hukumar ya cigaba da bayanin cewa mafi akasarin wadanda da hukumar ta kama bisa zargin rashawa basu taba karyata kasancewarsu da hannu a zargin da ake yi a kansu ba.

Da ya samu wakilcin kakakin hukumar, Wilson Uwujaren, a taron yaki da rashawa a Kaduna, yace hukumar bata sanya siyasa cikin lamarinta ba.

KU KARANTA KUMA: Daukaka kara: Alkalai 7 da zasu saurari karar Atiku a kotun koli

A wani labarin kuma Legit.ng ta rahoto a baya cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin ma'aikata (ICPC) ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shugaban hukumar kafafen sadarwa na kasa (NBC), Ishaq Modibbo Kawu, da sauran wasu ma'aikatan gwamnati 32 da ake tuhuma da laifin rashawa a gaban kotu.

Hukumar ICPC, wacce ta gurfanar da ma'aikatan, ta ce ya kamata gwamnatin tarayya ta dakatar da su har zuwa lokacin da za a kammala shari'a a kansu.

Kazalika, ICPC ta bukaci gwamnati ta yi amfani da dokokin aiki domin hukunta sauran ma'aikatan gwamnati da kotu ta tabbatar da samunsu da laifi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel