Cin hanci: ICPC ta bukaci FG ta dakatar da shugaban hukumar NBC, Modibbo Kawu, da sauran ma'aikata 32

Cin hanci: ICPC ta bukaci FG ta dakatar da shugaban hukumar NBC, Modibbo Kawu, da sauran ma'aikata 32

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin ma'aikata (ICPC) ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shugaban hukumar kafafen sadarwa na kasa (NBC), Ishaq Modibbo Kawu, da sauran wasu ma'aikatan gwamnati 32 da ake tuhuma da laifin rashawa a gaban kotu.

Hukumar ICPC, wacce ta gurfanar da ma'aikatan, ta ce ya kamata gwamnatin tarayya ta dakatar da su har zuwa lokacin da za a kammala shari'a a kansu.

Kazalika, ICPC ta bukaci gwamnati ta yi amfani da dokokin aiki domin hukunta sauran ma'aikatan gwamnati da kotu ta tabbatar da samunsu da laifi.

Bukatun hukumar na kunshe ne a cikin wata wasika da ta aika zuwa ofishin sakataren gwamnatin tarayya, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

ICPC ta ce yanzu haka ta gurfanar da ma'aikata 33 bisa tuhumarsu da aikata laifukan cin hanci, karyar takardun karatu, bayar da bayanan karya, hada baki domin satar kudin gwamnati da kuma almubazzaranci da dukiyar al'aumma.

Laifukan ma'aikatan, a cewar ICPC, sun ci karo da dokokin ma'aikatan gwamnati a Najeriya.

DUBA WANNAN: Gwamnonin arewa 4 da har yanzu kotu bata yanke hukunci a kan karar cin zabensu ba

Ma'aikatar lafiya ce a kan gaba wajen yawan ma'aikatan da hukumar ICPC ta bukaci a dakatar daga bakin aiki.

Kazalika, hukumar ta bukaci a dakatar da ma'aikata uku a ma'aikatar lantarki, aiyuka da gidaje da karin wasu ukun a hukumar tsaro ta NSCDC (Civil defence).

Akwai ma'aikata guda biyu da ICPC ta bukaci a dakatar a ma'ikatun gwamnatin tarayya da suka hada da; ofishin babban akawu na kasa, ma'ikatar kula da birnin tarayya (FCTA), ma'aikatar kimiyya da fasaha ta tarayya da kuma ma'aikatar harkokin kasashen waje.

ICPC ta mika sunayen ma'aikatan da take bukatar a dakatar a ma'aikatar harkokin cikin gida, ma'aikatar kula da muhalli ta tarayya, hukumar gidaje ta tarayya, hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin tarayya, rundunar soji, ofishin jihar Bayelsa da ke Abuja da NBC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel