Ta Allah ta yi: Cutar shawara ta halaka wani gagararren mai garkuwa da mutane a Zamfara

Ta Allah ta yi: Cutar shawara ta halaka wani gagararren mai garkuwa da mutane a Zamfara

Wani gagararren dan bindiga daya shahara wajen satar mutane tare da yin garkuwa dasu a jahar Katsina da Zamfara, Alhaji TK ya gamu da ajalinsa a dalilin barkewar cutar shawara, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cutar shawara ce ta yi ajalin TK tare da mukarrabansa guda 11, inda ta kara da cewa TK yana da yara yan bindiga sama da 200 da suka mamaye dajin Birnin Gwari, Sabuwa, Faskari, Danmusa, Jibiya har zuwa Nijar.

KU KARANTA: Duniya ta jinjina ma Buhari game da N-Power, ta karrama matar da ta kirkiro tsarin

A yan kwanakin baya an samu barkewar cutar shawara a jahohin Bauchi da Kano, inda har aka samu mace macen wasu mutane, rahotanni daga majiya mai sika sun bayyana cewa TK ya mutu ne bayan kamuwa da cutar shawarar, haka zalika wani na hannun damansa, Alhaji Auta ya mutu tare da matarsa da yayansa biyu.

“A zaman tattaunawa da muka mun kirga gawarwakin yan bindiga guda 12 da suka mutu a cikin sati daya, duk da yake ma’aikatan kiwon lafiya sun bayyana sababin mutuwarsu a matsayin shawara, mu muna ganin karfin Al-kunuti ne kawai.” Inji Rabe Kabir, mazaunin kauyen Kaiga.

Rahotanni sun kara da cewa jama’an kauyukan Kaiga, Malamai, Dufa Dan Kamtsa, Dufan Mato, Lailaito da Dandire sun yi ta murna a karshen makon data gabata bayan samun labarin mutuwar miyagun.

TK na daga cikin kusoshin yan bindiga da gwamnatin Zamfara ke tattaunawa dasu don yin sulhu, sai dai na kusa dashi sun tabbatar da cewa bai bar satar mutane ba, kuma tsohuwar gwamnatin Yari ce ta gina masa gida ta sanya masa wuta mai amfani da hasken rana, ta gina masa asibiti da kuma makaranta, duk a kauyensa na Ajjah.

“Duk da tattaunawar sulhun, TK ya sayi bindigar G3, da bamabamai guda 5 da yake shirin amfani dasu, shi da kansa ya karbo makaman kwanaki biyar kafin mutuwarsa.” Inji majiyar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel