The Best: Ahmed Musa ya zabi Lionel Messi a matsayin babban ‘Dan kwallon Duniya

The Best: Ahmed Musa ya zabi Lionel Messi a matsayin babban ‘Dan kwallon Duniya

A jiya Litinin, 23 ga Watan Satumban 2019 ne kungiyar kwallon kafa na Duniya, FIFA, ta bayyana Gwarazan wannan shekara inda aka bayyana Koci da jerin ‘Yan wasan da su ka fi kowa fice.

Lionel Messi ne ya lashe kyautar Maza a Duniya, inda ‘dan wasa baya Virgil Van Dijk ya biyo shi a baya. Babban ‘Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ne ya zo na uku a wannan shekarar ta bana.

Bayan an kammala bikin bada kyaututtukan a jiya, kungiyar FIFA ta bayyana yadda masu rike da kambun kasashen Duniya su ka kada kuri’arsu. Ana ba Kyaftin damar zaben manyan ‘yan wasa 3.

Shi dai Kyaftin din Super Eagles na Najeriya, Ahmed Musa, ya zabi Lionel Messi ne a matsayin babban ‘dan wasan bana. Kuri’arsa ta biyu kuma ta tafi ne wajen Cristiano Ronaldo na Portugal.

Kamar dai yadda alon na FIFA ya nuna, ‘Dan wasan gaban na Najeriya mai taka leda yanzu a kasar Saudiyya, Ahmed Musa, ya zabi Takwaransa na Nahiyar Afrika, Mo Salah ne a matsayin na uku.

KU KARANTA: Tauraron Super Eagles da ke wasa a Ingila ya bar kazamin tarihi

Ko da Messi ya zo na daya a Duniya, sai dai ba yadda Musa ya kada kuri’arsa ne aka raba kyaututtukan ba domin kuwa V. Dijk ne ya zo na biyu, yayin da Ronaldo ya rufe sahun ukun fari.

Wannan ne karo na shida da Tauraron na Barcelona ya lashe wannan kyauta a Duniya. Hakan na nufin Messi ya sha gaban babban Abokin hamayyarsa Ronaldo wanda ya lashe kyautar so biyar.

Kyaftin din kasar Faransa, Hugo Lloris, shi ma ya zabi Lionel Messi ne sannan Cristiano Ronaldo a na biyu. Lloris ya rufe kuri’arsa da Matashin ‘dan wasan gaban kasarsa watau Kylian Mbappe.

Harry Kane mai rike da kambun Ingila ya zabi Lionel Messi ne, sai kuma Virgil Van Dijk, sannan Ronaldo a na uku. A karshe Messi ya samu maki 46, Van Dijk 38 sai Ronaldo kuma mai maki 36.

‘Yan wasan Liverpool, Mohamed Salah da Sadio Mane ne su ka zo na hudu da biyar a Duniya. Masu horas da ‘yan wasa da kuma ‘Yan jarida su ne ragowar wadanda ke shiga wannan zabe.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel