Yanzu Yanzu: Kotu tayi umurnin sakin Omoyele Sowore

Yanzu Yanzu: Kotu tayi umurnin sakin Omoyele Sowore

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umurnin sakin jagoran zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore, zuwa ga Femi Falana, wanda ya zama dole ya gabatar dashi a duk lokacin da kotu ke neman shi.

Kotun a hukuncin da ta yanke a ranar Talata, 24 ga watan Satumba ta umurci Sowore da ya gabatar da takardun tafiyarsa cikin sa’o’i 48 da yanke hukuncin.

Da farko mun ji cewa kotun ta soke bukatar hukumar tsaro na sirri (DSS) na ci gaba da tsare mawallafin jardar SaharaReporters kuma jagoran zanga-zangar RevolutionNow, Omoyele Sowore.

Hakan ya biyo bayan janye bukatar da wani lauyan kasar yayi.

Lauyan Sowore, Femi Falana, ya bukac kotu da tayi umurnin sakin wanda yake karewa ba tare da bata lokaci ba tunda lauyan gwamnati baida ra’ayn ganin an cigaba da tsare shi.

Sai da kuma lauyan DSS, ya kalubalanci bukatar sakin nasa ta fatar baki cewa an riga an shigar da kara inda ake zargin Sowore da cin amanar kasa wanda ya kasance babban laifi.

An kama Sowore a ranar 3 ga watan Agusta, kwanaki biyu kafin zanga-zanga juyin juya hali kan zargin kokarin tunkudar da zababben gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Ta leko ta koma: Kotun zabe ta tsige yan majalisa 2 na APC, tayi umurnin maye gurbinsu da yan PDP

Mai karar na neman kotu ta hana ma wanda ake kara beli sakamakon sabon tuhumar da ake akansa.

Da yake martani lauyan Sowore yace an janye karar beli sannan cewa an janye bukatar lauyan me kara na cigaba da tsare shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel