Peter Obi ya fadawa Chris Ngige babu yadda ka iya da abin da na bari a Jihar Anambra

Peter Obi ya fadawa Chris Ngige babu yadda ka iya da abin da na bari a Jihar Anambra

‘Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar hamayya ta PDP a zaben 2019, Peter Obi, ya nemi Ministan kwadagon Najeriya, Dr. Chris Ngige, da ya daina yunkurin ci masa mutunci.

Peter Obi yake cewa kokarin da Chris Ngige ya ke yi na bata masa sun aba zai kai ko ina ba. A madadin haka, Obi ya nemi Ministan ya maida hankalinsa wajen yi wa kasa aikin da aka ba shi.

A cewar tsohon gwamna Peter Obi, aikin da Chris Ngige ya yi a lokacin ya na gwamna, bai isa ya goge irin dinbin ayyukan da shi ya yi ba. Dukkaninsu dai sun taba mulkar jihar Anambra a baya.

Mista Peter Obi ya yi wannan jawabi ne bakin Hadimansa na yada labarai, Valentine Obienyem. Mista Obienyem ya fitar da wannan jawabi ne a jiya Ranar Litinin, 23 ga Watan Satumban 2019.

KU KARANTA: Malaman Makaranta sun yi wata da watanni babu albashi a Jihar Kogi

A jawabin na Peter Obi, ya bayyana cewa Ngige ya dage da karfi da yaji sai ya soke sa, yayin da shi kuwa ko a lokacin yakin neman zabe bai tsaya sukarsa ba, sai dai ma ya yabawa ‘dan kokarinsa.

Hadimin tsohon gwamnan ya yi kaca-kaca da yadda Ngige ya lissafo hanyoyin Abatete-Nteje-Aguleri-Otuocha da irin su titin Igboukwu-Ezenifite-Umunze da na Iseeke a matsayin ayyukansa.

Obi ya ce shi ne ya yi mafi yawan wadannan hanyoyi da Ngige ya ke ikirarin aikinsa ne inda ya kara da cewa kashi 90% na titun da Ngige ya ambata ya yi, su na cikin karamar hukumar sa ne.

‘Dan takarar na PDP a zaben 2019 yake cewa babu hadi tsakanin shi da Ngige ta ko ina, daga bangaren ilmi, kiwon lafiya, kasuwanci zuwa abubuwan more rayuwa, babu abin da Ngige ya yi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel