Yanzu-yanzu: Atiku ya shigar da Buhari kara kotun koli

Yanzu-yanzu: Atiku ya shigar da Buhari kara kotun koli

- Atiku Abubakar da jam'iyyar Peoples Democratic Party sun shigar da kara kotun kolin Najeriya kan hukuncin da kotun zaben shugaban kasa ta yanke

- Atiku ne dan takarar jam'iyyar PDP a zaben 2019 inda shugaba Muhammadu Buhari ya dokesa

- Lauyoyin PDP sun bukaci kotun koli ta yi watsi da shari'ar kotun zabe saboda akwai kura-kurai cikin sharii'ar

Dan takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, Atiku Abubakar, da jam'iyyarsa sun shigar da kara kotun kolin tarayya kan hukuncin da kotun zaben shugaban kasa ta yanke.

Lauyan PDP, Mike Ozekhome SAN, ne ya bayyana hakan. This Day ta bada rahoto.

A cewar Ozekhome, kotun zabe karkashin jagorancin Alkali Garba Mohammed, ta yi kuskure wajen tabbatar da nasarar shugaba Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Shari'ar Ganduje da Abba: PDP ta gaza gabatar da sahihan hujjoji - Lauyan INEC

Za ku tuna cewa a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, 2019 kotun zaben shugaban kasa na alkalai biyar sun yi ittifakin cewa karar da Alhaji Atiku Abubakar ya shigar babu kanshin gaskiya cikinta kuma sunyi watsi da ita.

Bayan kwashe akalla sa'o'i 8 a kotu, Alkali Garba Mohammed, ya tabbatar da shugaba Muhammadu Buhari matsayin zakaran zaben 23 ga Febrairu 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel