Dalilin da yasa likitoci ke barin Najeriya - MDCAN

Dalilin da yasa likitoci ke barin Najeriya - MDCAN

Kungiyar Likitocin Najeriya (MDCAN) reshen Asibitin Jami'ar Ibadan a ranar Litinin ta nuna damuwarta kan yadda takwarorinsu ke ficewa suna barin Najeriya zuwa kasashen waje.

Yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, shugaban na MDCAN, Dr Dare Olulana ya ce kungiyarsa na fama da matsalar yadda takwarorinsu ke ficewa kasashen waje kamar yadda PUNCH ta ruwaito.

Ya ce, "Abin bakin ciki ne saboda lokacin ana bamu horo, marasa lafiya ba su biyan kudi daga aljihunsu. Ana biya musu kudin kulawa da ya kai dubban nairori.

"Amma a yanzu, kana komawa gida ne cikin bacin rai, baka samun gamsuwa cikin aikinka saboda wasu lokutan wadanda ka ke kulawa da su sukan mutu saboda ba su da kudin da za su biya na magani.

DUBA WANNAN: Yadda yarjejeniya da aka kulla tsakanin tsohon gwamnan PDP da Buhari kafin zabe ta samu tangarda

"Hakan yasa wasu likitoci da yawa ke ficewa daga kasar domin babu dadi wadanda ka ke kula da su suna mutuwa a hannun ka. Kana son kayi aiki ne a kasar da ke daraja aikinka da karrama ka."

Ya kara da cewa, "Hakan na faruw a kullum; likitoci suna barin kasar zuwa inda za su samu albashi mai tsoka. A kwanaki biyu da suka wuce, na ga wasu takwarorin mu da suka kira suka ce sun koma Ingila inda suke aiki a matsayin kwararru.

"A Legas, kimanin likitoci 60 suna bar aiki da gwamnatin jihar Legas duk wata banda wadanda ke aiki a asibitocin kudi.

"Ba mu da kididigan wadanda ke barin aiki a Ibadan amma ina fada maka suna da yawa da ke niyyar barin aiki, wasu na cika fom suna jiran dama ta samu domin su fice."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel