Matashi ya mutu yayin wanka a kududufi a Kano

Matashi ya mutu yayin wanka a kududufi a Kano

- Matashi mai shekaru 20 ya mutu yayin da ya tafi wanka a kududufi a jihar Kano

- An sanar da jami'an kwana-kwana cewa an hangi gawar dan adam amma ko da suka iso sun tarar ya mutu

- A halin yanzu ana gudanar da bincike kan yadda lamarin ya afku da nufin kiyaye afkuwar haka a gaba

Wani matashi mai shekaru 20, Sani Iliyasu ya mutu yayin wanka a wani kududufi da ke Bachirawa a Darerawa a karamar hukumar Ungogo na jihar Kano kamar yadda mai magana da yawun hukumar Kwana-kwana na jihar Kano, Malam Saidu Mohammed ya bayyana.

Mohammed ya tabbatar da afkuwar lamarin yayin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Kano inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi yayin da marigayin ya tafi wanka.

"Wani malam Abdulrahman Adamu ya kira mu a waya misalin karfe 12.45 na rana inda ya ce an gano gawar Iliyasu na yawo a cikin kududufi.

DUBA WANNAN: Yadda yarjejeniya da aka kulla tsakanin tsohon gwamnan PDP da Buhari kafin zabe ta samu tangarda

"Da samun bayanin, nan take muka tura jami'an mu masu ceto mutane inda suka iso wurin misalin karfe 1.00 na rana kuma muka ciro gawar Iliyasu daga kududufin."

Mohammed ya ce an mika gawar mamacin ga shugaban mazabar Zangon Barebari, Alhaji Ahmed Isa.

A baya, NAN ta ruwaito cewa wani yaro mai shekaru 16, Shahid Lawal shima ya mutu yayin da ya ke wanka a wani kududufi da ke Bacharawa Ramin Kasa da ke karamar hukumar Fagge a Kano a ranar 5 ga watan Satumba.

Sai dai har yanzu ana gudanar da bincike kan mutuwar matasan biyu a cewar Mohammed.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel