Ta leko ta koma: Kotun zabe ta tsige yan majalisa 2 na APC, tayi umurnin maye gurbinsu da yan PDP

Ta leko ta koma: Kotun zabe ta tsige yan majalisa 2 na APC, tayi umurnin maye gurbinsu da yan PDP

Kotun sauraron kararrakin zabe a Yola, jihar Adamawa ta tsige yan majalisa biyu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kotun ta tsige Shuaibu Langa na jam’iyyar APC bisa zargin mallakar satifiket na bogi.

A cewar kotun, an soke zaben Mista Langa a matsayin dan majalisa mai wakiltan yankin Arewacin Mubi a majalisan dokokin jihar Adamawa, a ranar Litinin saboda ya gabatar da takardan karatu na bogi.

Kotun wacce S. Akabi ke jagoranta, ya ba hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) umurnin baiwa Suleiman Vokna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) takardan shaidar lashe zabe.

Yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, Mista Langa ya sha alwashin neman hakkinsa.

Kotun zaben ta kuma soke zaben Musa Boror, mamba na APC mai wakiltan mazabarMubi ta Kudu akan "amsa nunaye uku da suka sha bambam."

Kotun ta zarge shi da yin amfani da sunaye uku, Musa Umar Bororo a maimakon “Musa Umar” wanda ya kasance sunan da takardun da ya gabatar ma hukumar INEC ke dauke da shi.

Musa Dirbishi na jam’iyyar PDP ne ya maka Mista Bororo a kotu.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2023: Fastocin El-Rufai, Tinubu da Oshiomhole sun kawo kace nace a Najeriya

Kotun ta umurci hukumar INEC da ta baiwa Mista Dirbishi takardan lashe zabe.

Mista Bororo har ila yau ya sha alwashin kalu balantan hukuncin kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel