Duniya ta jinjina ma Buhari game da N-Power, ta karrama matar da ta kirkiro tsarin

Duniya ta jinjina ma Buhari game da N-Power, ta karrama matar da ta kirkiro tsarin

Gidauniyar Schwab, wani reshe na majalisar tattalin arziki ta duniya ta jinjina ma shugaban kasa Muhammadu Buhari game da amfani da tsarin tallafa ma matasa marasa aikin da gajiyayyu tare da karrama Hajiya Maryam Uwais, matar da ta kirkiri tsarin.

Hajiya Maryam Uwais ce shugaban sashin kula da tsare tsaren tallafin gwamnati da suka hada da N-Power, bashin Tradermoni, ciyarwa a makarantun firamari da kuma kananan basussuka ga mata da masu sana’o’in hannu.

KU KARANTA: Kotu ta yi ‘waje road’ da dan majalisan APC dake amfani da takardun karatu na bogi

Duniya ta jinjina ma Buhari game da N-Power, ta karrama matar da ta kirkiro tsarin
Uwais
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta ruwaito Uwais na daga cikin mutane 40 da gidauniyar ta karrama a ranar Lahadi, 22 ga watan Satumba a New York, saboda kwazon da suka nuna wajen kirkirar wasu tsararraki da zasu kawo sauki ga al’ummomin duniya gaba daya.

Shugaban sashin kula da tsare tsaren tallafi na gidauniyar, Justice Bibiye ya bayyana cewa sun karrama manyan masu kamfanoni, shuwagabannin hukumomin gwamnati da kuma masu kananan masana’antu dake taimakawa wajen kawar da matsalolin al’umma.

Ita ma a nata jawabin, Maryam Uwais, wanda bata samu halartar taron ba ta bayyana cewa: “Na ji dadi da wannan karramawa daga kasashen duniya, hakan ya nuna cewa a shirye Najeriya take domin rage talauci a tsakanin jama’anta.

“Hakan kuma tabbaci ne na cewa yan majalisunmu, gwamnoninmu da kuma abokan huldar gwamnatin tarayya, suma a shirye suke su tallafa ma marasa karfi, saboda akwai kyakkyawar alakar aiki tsakanin bangarorin wanda hakan ya kawo nasarar da ake samu wajen cimma manufa.” Inji ta.

Daga karshe ta gode ma Allah daya bata damar yi ma kasarta hidima, sa’annan ta gode ma mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo daya jagoranci muhimmin aikin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel