An damke wanda ya kashe kwamandan Sojoji a Jaji

An damke wanda ya kashe kwamandan Sojoji a Jaji

A ranar Litinin, Bayanai sun fara bayyana kan kisan Kwamandan makarantar sojin da aka kashe, Oluwayemisi Ogundana, a Jaji a makon da ya gabata.

Bincike ya nuna cewa marigayiyar ta gamu da ajallinta ne a hannun kwartonta wanda ma'aikacin makarantan sojin ne.

Kwarton kuma wanda ake zargi da kisan, Simon Bernard, ya kasance shugaban kungiyar malamai da iyayen yaran makaranta wato PTA. Ya ce ya aikata wannan laifi ne don kwamandar ta tsogeshi daga matsayinsa.

A cewar Vanguard, Bernard ya ce bayan ta tsigeshi daga matsayinsa, ta yi masa alkawarin cewa za ta bashi kudi N2.5million amma bata cika ba.

Bayani kan yadda aka damkeshi, majiya mai karfi ya bayyana cewa jami'an hukumar sojin sama ne suka damkeshi ta hannun wani direba.

KU KARANTA: Shari'ar Ganduje da Abba: PDP ta gaza gabatar da sahihan hujjoji - Lauyan INEC

An ga wani direba a Jaji da motar marigayiyar kirar Toyota Highlander, ba tare da bata lokaci ba jami'an sojojin suka damkeshi a Kaduna.

Yayin bincike, direban ya bayyana cewa wani mutum ne ya bashi motar domin ya sayar masa. Bayan kwanaki ana neman mutumin, sai aka gano Mista Bernard ne, wanda malamin makarantar sakandaren Sojin ne.

Ba tare da bata lokaci ba aka damke shi.

Yayin bincike, Bernard tabbatar da cewa lallai shi ya kashe matar a kauyen Angwan Loya dake Jaji, jihar Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel