An gurfanar da likitoci biyu a gaban kotu sakamakon ajalin mace mai juna biyu

An gurfanar da likitoci biyu a gaban kotu sakamakon ajalin mace mai juna biyu

- Kotun sauraron kararraki ta kungiyar likitocin Najeriya ta gurfanar da wasu likitoci biyu

- Ana zarginsu ne da sakaci tare da ganganci wanda ya jawo halakar wata mata mai juna biyu

- An kirkiro da kotun ne don hukunta likitocin kasar nan masu karantsaye ga dokokin aikinsu

Likitocin biyu daga cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Asaba sun gurfana a gaban kotun sauraron kararraki ta kungiyar likitocin Najeriya.

Likitocin biyu, Iyiola Adewale da Adigab Onodjohwoyovwe, an zargesu ne da sakaci tare da ganganci akan aikinsu wanda hakan ya kai ga rasuwar majinyaciya a karkashin kulawarsu.

Lauyan mai kara, Nasiru Aliyi, ya sanar da kotun a ranar Litinin cewa a ranar 7 ga watan Maris, 2017, likitocin sunyi sakaci da ganganci yayin da suke aiki wanda hakan ya jawo rasa rayuwar wata mace mai juna biyu, Rita Uchebuego.

Kamar yadda ya ce, ana zarginsu da kin dubata yadda ya dace a halin da ta tsinci kanta a ciki.

Aliyu ya ce, laifinsu abin hukuntawa ne a karkashin sashi na 16 a dokar kungiyar likitoci ta kasa.

Amma kuma, wadanda ake karar sun musanta zargin da ake musu.

KU KARANTA: DPR ta rufe gidajen mai 12 a jihohin Sokoto da Kebbi

Shugaban kotun, Farfesa Abba Hassan, ya daga sauraron karar zuwa 24 ga watan Satumba inda zai yanke hukunci.

An kirkiro da kotun ne don hukunta likitocin kasar nan.

Wannan ne zaman kotun na 3 a cikin shekarar 2019 kuma har ta yankewa wasu likitocin hukunci a zamanta na biyu sakamakon rashin da'a ga dokokin aikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel