Toh fah: Masu garkuwa da mutane sun sace wani dan kasuwa a jihar Sokoto

Toh fah: Masu garkuwa da mutane sun sace wani dan kasuwa a jihar Sokoto

- A ranar Litinin ne mazauna kauyen Sabaru suka fada cikin tashin hankali da fargaba

- Hakan ya biyo bayan tsinkayar kauyen da wasu 'yan bindiga suka yi tare da awon gaba da wani Dan kasuwa

- Mazauna yankin sun fada alhini da fargaba saboda kauyen bashi da nisa da cikin garin Dange

Wasu 'yan bindiga da ake zarginsu da garkuwa da mutane sun sace wani Dan kasuwa mai suna Tukur Sabaru, a kauyen Sabaru da ke karamar hukumar Dange/Shuni da ke jihar Sokoto.

Majiya ta tabbatarwa da manema labarai cewa an jefa kauyen cikin alhini a ranar Litinin sakamakon tsinkayar kauyen da 'yan bindigar suka yi tare da awon gaba da Dan kasuwan.

Wata majiya daga iyalan Dan kasuwan ta sanar da TVCNews cewa an sace Dan kasuwan ne da karfe 8:15 na dare a yayin da ya dawo daga kasuwan.

KU KARANTA: Tubabban 'yan ta'addan jihar Zamfara sun mika bindigogi 100 ga jami'an tsaro

Tsoro da fargaba sun kama mazauna yankin Inda suka nuna damuwarsu sakamakon rashin tazarar Sabaru da ainihin cikin garin.

Majiya daga hukumar 'yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin ga TVCNews.

Amma kuma jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, ASP Sadiq Abubakar, ya ce har yanzu babu cikakken bayani game da harin.

Ya kara da cewa 'yan sanda na cigaba da binciken lamarin kuma zasu sanar da manema labarai don yaye fargabar da mazauna yankin suka fada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel