An kama saurayi da budurwa da su kayi kutse asusun NHIS suka sace N60m

An kama saurayi da budurwa da su kayi kutse asusun NHIS suka sace N60m

- 'Yan sanda sun kama wasu masoya biyu da aka ce sun yi kutse cikin asusun NHIS

- Ana zargin masoyan da dace zunzurutun kudi naira miliyan 60

- Rundunar 'yan sandan ta ce za ta gurfanar da masoyan biyu a gaban kotu da zarar ta kammala bincike

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta kama wasu masoya, Tunde Ogunseye da sahibarsa Funmiayo Oyelaja da aka ce sunyi kuste cikin asusun Hukumar Ishorar Lafiya ta Kasa (NHIS).

Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan sanda sun dade suna neman masoyan da suka sace naira miliyan 60 ruwa a jallo.

An ruwaito cewa masoyan sun tsere zuwa kasar Ghana bayan aikata laifin.

A cewar 'yan sanda, "Oyelaja tayi amfani da damar da ta ke da shi na aiki da kamfanin adana bayanan lafiya mai suna Clearline International Limited da ke Legas inda tayi kuste cikin asusun na NHIS."

DUBA WANNAN: Yadda yarjejeniya da aka kulla tsakanin tsohon gwamnan PDP da Buhari kafin zabe ta samu tangarda

A rahoton da ta bayar na amsa laifinta, Oyelaja ta ce: "Nayi aiki da Clearline International Limited daga shekarar 2014 zuwa 2019. Aikin mu shine sadar da asibitoci da hukumar NHIS. Idan NHIS ta bamu kudi mu biya asibitoci, mu kan rage wani kaso cikin kudin kuma ba mu mayarwa asusun NHIS."

A bangarensa, Ogunseye ya ce ya san cewa masoyiyarsa na aikata wannan damfarar amma ya ce ba shi da hannu ciki.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Legas Zubairu Muazu ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifin a gaban kuliya.

Kazalika, rundunar 'yan sanda sun kama wani matashi Emmanuel O. Isreal da ke ikirarin cewa shi dan hamshakin mai kudi, Sanata Ned Nwoko ne a jihar Rivers.

An ruwaito cewa Isreal ya dade yana damfarar mutane a kafar sada zumunta na Facebook, Instagram, Twitter da Whatsapp.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel