Zaben 2023: Fastocin El-Rufai, Tinubu da Oshiomhole sun kawo kace nace a Najeriya

Zaben 2023: Fastocin El-Rufai, Tinubu da Oshiomhole sun kawo kace nace a Najeriya

Shekaru hudu kafin zaben Shugaban kasa na 2023, batun wanda zaii gaji Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen zama Shugaban Najeriya na gaba ya fara karade shafukan sadarwa, inda tuni manyan hotunan wasu yan siyasa ya fara shawagi a wasu manyan biranen kasar.

Manyan hotunan wadanda aka gano a wasu yankunan Najerya sun hada da na babban jigon jam’yyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da kuma Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole.

A birnin Kaduna, an gano fosta mai kamar haka; ‘El- Rufai 2023 (Mai Aiki) for President, Federal Republic of Nigeria’, wanda hakan ne nuni ga neman kujerar shugabancin kasa, kuma kungiyar matasan arewa c eta nauki nauyin buga wadannan hotuna kamar yadda aka gano a wasu yankunan jihar a ranar Lahadi.

A Ikeja, an gano babban hoton Tinubu a daiidai tashar ‘Ikeja Along’ dauke da rubutun ‘BAT 2023’, koda dai a sauke hoton.

A wasu yankunan Abuja ma, an gano hotunan Oshiomhole, da el-Rufai a matsayin abokan takara a gine-ginen gwamnati.

Akan fostan an rubuta, ‘Mandate 2023’, an tabbaya cewa kungiyar makiyayan Miyetti Allah ne suka dauki nauyin tallan.

Koda dai babu daya daga cikin yan siyasa uku da ya fito karara ya kaddamar da kudirinsa na takara, akwai rade-radin cewa suna shirin takara amma suna amfani da yan kasheninsu wajen gabatar da kudirinsu.

Babban sakataren kungiyar Arewa, Anthony Sani, ya bayyana hotunan a matsayin illa ga damokradiyyar Najeriya, cewa gwamnati mai ci tayi wuri da za a fara zance shugabanci na gaba.

KU KARANTA KUMA: Kuma dai: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 13 a hanyar babban titin Abuja zuwa Kaduna

Hakazalika babban sakataren kungyar Afenifere, Yinka Odumakin, ya koka akan bayyanar kayan kamfen kan zaben Shugaban kasa na 2023.

Odumakin yace, koda dai yan siyasa na da dammar yin kamfen, kamata yayi su ci gaba da bayar da gudunmawarsu wajen kawo chanjin da suka yiwa yan Najeriya alkawari wanda a cewarsa, yan Najeriya basu gani ba a kasa har yanzu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel