Tafkin Chadi: Jawaban Buhari a taron Majalisar Dinkin Duniya

Tafkin Chadi: Jawaban Buhari a taron Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake gabatar da muhimmiyar bukata ta magance matsalar kafewa da tafkin Chadi ke ci gaba da fuskanta a sanadiyar sauyin yanayi.

Babu shaka kimanin mutane miliyan 40 da ke kewaye a gabar tafkin na samun arzikin kasar noma da kuma kamun kifi wato su, lamarin da a halin yanzu suke fuskantar barazanar kafewar babban ruwan.

Muryar Duniya wato RFI Hausa ta ruwaito cewa, furucin shugaban kasa Buhari ya zo ne a yayin halartar taron majalisar Dinkin Duniya karo na 74 a tarihi, inda ya ce tsukewar da tafkin Chadi ke yi illa ce ga mutanen da suka dogara da shi wajen noma da sana'ar su.

Buhari ya jaddada bukatar hadin kan sauran shugabannin kasashen duniya domin magance wannan barazana da ta tunkaro al'ummomin da suka dogara a kan tafkin.

Hakazalika shugaban kasar ya ce Najerita za ta ci gaba da hadin kai da sauran kasashen duniya da manufar dawo da martabar tafkin domin inganta rayuwar jama'ar da ke kewaye da shi gami da samar da tsaro.

KARANTA KUMA: Tinubu ba zai zama shugaban kasa ba, 'dan Arewa ne zai ci gajiyar mulki a 2023 - Yerima

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban kasa Buhari a yayin taron ya shaida wa zauren majalisar dinkin duniya cewa, zaben dan Najeriya, Farfesa Tijjani Bande a matsayin sabon shugaban majalisar ba zabe ne na tumun dare ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel