Tinubu ba zai zama shugaban kasa ba, 'dan Arewa ne zai ci gajiyar mulki a 2023 - Yerima

Tinubu ba zai zama shugaban kasa ba, 'dan Arewa ne zai ci gajiyar mulki a 2023 - Yerima

- Shugaban kungiyar tuntuba ta matasan Arewa, ya ce yankin Kudu maso Gabashin Najeriya zai goyi bayan dan takarar shugaban kasa da ya fito daga yankin Arewa a 2023

- Yerima ya jaddada cewa Arewa na bukatar sake samun wata damar a 2023 domin ya zamto sakayya ta kalubalen da suka tunkarar yankin a yanzu

- Shugaban kungiyar matasan yana da yakinin cewa, Bola Tinubu ba zai taba samun goyon baya ba koda kuwa ya yanke shawarar fito wa takarar shugaban kasa a 2023

Jagoran kungiyar tuntunba ta matasan Arewa, Yerima Shettima, ya ce babban zaben kasa na 2019 da ya gabata, wata manuniya ce da ta tabbatar da yankin Arewa zai ci gaba da samun rinjayen nasara sanadiyar yawan kuri'u masu zabe.

Da yake ganawa da wakilinmu, Eromosele Ebhomele, ta hanyar wayar tarho, Yerima yana da yakinin cewa, yankin Kudu maso Gabashin zai goyin bayan Arewacin kasar wajen samar da magajin shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben kasa na 2023.

A sanadiyar haka ya sanya Yerima ya nemi kanwa uwar gamin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, da ya jingine kudirin fitowa takarar shugabancin Najeriya matukar yana da niyyar hakan, da a cewarsa ba zai samu wani goyon baya ba.

KARANTA KUMA: Wasu hotunan tsohon shugaban kasa Barack Obama tare da iyalansa da baku taba gani ba

Shugaban kungiyar matasan ya ce akwai bukatar yankin Arewa ya ci gaba da riko da akalar jagoranci domin hakan ya zamto a matsayin wata babbar sakayya ta kalubalen da yankin yake fuskanta a yanzu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel