Bani da wata faduwar gaba kan barazanar tsige ni - Trump

Bani da wata faduwar gaba kan barazanar tsige ni - Trump

A wani rahoto da jaridar BBC Hausa ta wallafa a ranar 24 ga watan Satumban 2019, akwai yiwuwar za a tsige shugaban kasar Amurka, Donald Trump, bisa yunkurinsa na jan hankalin shugaban kasar Ukraine wajen kaddamar da bincike kan dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Democrat, Joe Biden.

Rahotanni na nuni da cewa, Donald Trump na neman gwamnatin kasar Ukraine ta kaddamar da bincike a kan Joe Biden wanda ya kasance tsohon mataimakin shugaban kasar a gwamnatin Barrack Obama.

A wani jawabi da Mista Trump ya gabatar cikin birnin New York, ya zargi 'yan jam'iyyar Democrat da kull masa tuggu ta bayan fage, inda yayin amsa tambayoyin manema labarai ya ce ko kadan ba ya da wani shakku kan barazanar tsige shi.

Takaddamar wannan lamari na zuwa ne a yayin da shugaban kasar Amurka ke zargin 'dan Joe Biden, Hunter Biden, da laifuka na rashawa. Hunter dai ya kasance daya daga cikin manyan ma'aikata masu daukar albashi mafi tsoka a wani babban kamfanin makamashi na kasar Ukraine, Burisma.

KARANTA KUMA: Hukumar NSCDC ta kama mahaifin da ya yiwa diyarsa fyade a jihar Borno

Ya zuwa yanzu, Mista Trump na ci gaba da fuskantar matsin lamba a kan ya fitar da bayanai game da wata tattaunawa da ta gudana tsakanin sa da shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ta hanyar wayar tarho.

Sai dai ko shakka babu shugaban na Amurka ya ce sun tattauna dangane da zargin rashawa da ake yiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden da kuma dansa Hunter, wanda ya shafe kimanin shekaru biyar yana aiki da kamfanin na kasar Ukraine.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel