Karancin mahalli na addabar mutanen Najeriya - Majalisar Dinkin Duniya

Karancin mahalli na addabar mutanen Najeriya - Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya wadda babu shakka ta kasance kanwa uwar gami, ta sake yi gargadin cewa, kasar Najeriya tana cikin jerin sahun kasashen duniya mafi muni wajen fama da matsananciyar matsala ta karancin gidaje.

A kiyasin da majalisar tayi, ta ce akalla fiye da kashe biyu cikin uku na 'yan Najeriya na zaune ne a mahallai irin na marasa karfi gami da rashin wadattun ababe na more rayuwa.

Kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito daga kamfanin dillancin labarai na Reuters, jami'ar Majalisar Dinkin Duniya mai sa ido kan samar da gidaje, Leilani Farha, ita ce ta bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai cikin babban birnin kasar nan na Tarayya.

A yayin kawo karshen binciken kwanaki goma da ta gudanar kan yanayin gidaje a manyan biranen Najeriya, Ms Farha ta alakanta annobar cin hanci da rashawa da ta yi kane-kane wajen samar da mahallai, lamarin da ta ce ana gina gidaje na alfarma wanda suka fi karfin mallakar mafi akasarin al'ummar kasar.

Hakazalika Ms Farha ta ce kimanin mutane miliyan 22 sun rasa muhallansu musamman a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, a sanadiyar kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram wadda ta daura damarar ta'addancin tsawon shekaru fiye da goma da suka gabata.

KARANTA KUMA: Gwamna Badaru ya nada mashawarta na musamman guda 15 a Jigawa

A wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, a halin yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari yana birnin New York na kasar Amurka, inda ya ke halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 74 a tarihi.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel