Kuma dai: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 13 a hanyar babban titin Abuja zuwa Kaduna

Kuma dai: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 13 a hanyar babban titin Abuja zuwa Kaduna

Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane 13 ne yan bindiga suka yi garkuwa da su a kauyuka biyu da ke hanyar babban titin Abuja zuwa Kaduna a tsakanin ranar Asabar da Litinin.

A cewar wata majiya, an sace mutane bakwai a ranar Asabar a Begiwa sannan aka yi garkuwa da wasu shida a ranar Litinin a kauyen Dutse, duk a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna, jaridar Punch ta ruwaito.

Majiyar wacce tayi magana akan sharadin boye sunanta, tace yan bindiga da muggan makamai sun mamaye garuruwan guda biyu a hanyar babban titin, sannan suna ta harbe-harbe tare da dauke mutanen zuwa wani wuri da ba a sani ba.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, majiyar tace har yanzu mutanen na a hannun wadanda suka yi garkuwa dasu domin cewa ba a bukaci kudin fansa ba akan sakin nasu.

An tattaro cewa mazauna garuruwan na zama ne cikin tsoro tun bayan afkuwar lamarin.

KU KARANTA KUMA: Ba ka tanadi abin da za ka fadawa Duniya a gaban UNGA ba; PDP ga Shugaba Buhari

Sunyi kira ga gwamnati da tayi gaggawan kawo masu agaji ta hanyar samar masu da ingantaccen tsaro a hanyar babban titin.

A halin da ake ciki, rundunar yan sandan jihar Kaduna bata rga ta tabbatar da lamarin ba domin a cewar majiyarmu kakakin rundunar, DSP Yakubu Sabo baya daukar wayarsa, sannan kuma bai amsa sakon waya da aka tura masa ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel