Ba ka tanadi abin da za ka fadawa Duniya a gaban UNGA ba; PDP ga Shugaba Buhari

Ba ka tanadi abin da za ka fadawa Duniya a gaban UNGA ba; PDP ga Shugaba Buhari

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, ta koka game da tafiyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi zuwa gaban babban zauren majalisar dinkin Duniya a kasar waje.

PDP ta ke cewa abin takaici ne ace shugaban Najeriyar zai tafi taron majalisar dinkin Duniya ba tare da ya tattaro wasu ayyanannun manufofi da hanyoyi da dabarun da zai taimakin Najeriya ba.

Sakataren yada labaran jam’iyyar adawar na kasa, Mista Kola Ologbondiyan, a wani jawabi da ya fitar ya ce shugaban kasa Buhari ya samu damar fita yawon gantali ne kurum a kasashen Duniya.

Kola Ologbondiyan ya ce Buhari ya halarci muhimmin taro da manyan shugabannin kasashen Duniya ba tare da wani tanadi game da Najeriya, ya nuna cewa ba cigaban kasar ba ce a gabanshi.

“Abin kokawa ne ace a lokacin da sauran shugabanni su ke zuwa taro da manufofi da kudirori da za su bunkasa cigaban kasarsu da gogewarsu a Duniya, Buhari ya kama hanya ya tafi wayam.

KU KARANTA: Adesina da Dangote sun shiga wani kwamitin Majalisar dinkin Duniya

Kakakin na PDP ya kara da cewa wannan na nufin shugaban kasar Najeriyar zai je ya dawo ne a tutar babu. Ologbondiyan ya ke cewa kashin zargin murde zaben Najeriya ne ma a kan Buhari.

A cewar Ologbodiyan, shekaru hudu kenan a mulkin Buhari, ba a taba karuwa da damar da ake samu a wajen wannan babban taro ba, duk da dukiyar da ake batarwa domin halartar Najeriya.

Ya ce: “PDP ta na iya tuna yadda Buhari ya tafi babban taron Duniya kan cigaban Afrika da aka yi a Birnin Tokyo, a daidai lokacin da Takwaransa na Ghana, Nana Akufo-Ado, ya ci ribar taron.”

A wajen wannan taro da aka yi a Tokyo ne shugaba Nana Akufo-Ado ya sa hannu a wata yarjejeniya da Toyota da Suzuki domin su kafa kamfaninsu a kasar Ghana inji jam’iyyar ta PDP.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel