Ba za mu lamunci karantsaye da take doka ba a kasar nan, in ji shugaban alkalan Najeriya

Ba za mu lamunci karantsaye da take doka ba a kasar nan, in ji shugaban alkalan Najeriya

- Mai shari'a Tanko Muhammad, ya ce bangaren shari'ar kasar nan da ke karkashin ikonsa ba za ta lamunci rashin bin dokar kotu ba

- Babban alkalin ya sanar da hakan ne a taron bude sabuwar shekarar shari'a ta 2019 zuwa 2020

- Ya ce riko da kundin tsarin mulki a matsayin mafificiyar doka ita kadai ce mafita ga kowa, komai kuwa matsayinsa

Mai shari'a Tanko Muhammad, shugaban alkalan Najeriya, ya ce bangaren shari'a na kasar nan da ke karkashinsa zata riki kundin tsarin mulkin kasar nan a matsayin mafificiyar doka.

Ya ce shugabancinsa ba zai lamunci rashin biyayya ga dokoki ko hukuncin kotu.

Muhammad ya sanar da hakan ne a taro na musamman da ke nuna farawar sabuwar shekarar shari'a ta 2019 zuwa 2020. A taron ya rantsar da manyan lauyoyin Najeriya har 38.

Idan zamu tuna, an zargi gwamnatin Najeriya da rashin biyayya ga hukuncin kotu ko kuma zaben hukuncin da zata bi.

Muhammad ya ce taka tsan-tsan da doka shi ne jigon duk wata damokaradiyya a fadin duniya.

"Dole ne mu kiyaye doka a kowacce mu'amalarmu kuma mu tabbatar da an bi ta a kowanne mataki na gwamnati. Bin hakkin kowanne Dan kasa dole ne ga shari'a. Don haka, dole ne a bi kowacce dokar kotu."

"Babu wanda za a lamuncewa komai matsayinsa ko mukaminsa idan ya taka dokar kotu," in ji shi.

KU KARANTA: Idan kaji gangami, akwai labarai: Gwamnonin PDP 8 sunyi taro a jihar Rivers

Ya yi kira ga kowa da a nuna jajircewa wajen biyayya ga dokokin Najeriya.

"Kamar yadda muka sani, kin biyayya ga hukuncin kotu ko kuma take doka gayyatar tashin hankali ce kai tsaye. Wannan abu kwata-kwata bai dace ga damokaradiyya ba kuma zamu lamuncesa ba a karkashin mulkina na shugaban shari'a."

"Dole ne muyi aiki tukuru wajen ganin Najeriya ta zamo cikin kasashen sahun gaba da ke biyayya ga doka da kare hakkin 'yan kasa a kowanne fanni."

Ya ce ma'aikatar shari'ar da ke karkashinsa ta rungumi kimiyya don habaka bangaren shari'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel