BESAN: Malaman Makaranta sun roki Gwamna Bello ya biya su tarin albashinsu

BESAN: Malaman Makaranta sun roki Gwamna Bello ya biya su tarin albashinsu

Mun ji cewa malaman makarantun firamare da kananan sakandare fiye da 7000 a jihar Kogi su na bin gwamnatin jiharsu bashin albashi na akalla watanni takwas har zuwa tsawon watanni 39.

Ma’aikatan sun yi kira ga gwamna mai-ci, Yahaya Bello, ya taimaka ya biya wadannan kudi da ake bin gwamnatin jihar Kogi bashi. Malaman sun yi wannan kira ne bayan wani taro a jiya.

Kungiyar BESAN ta Ma’aikatan makarantan Najeriya sun yi wani zama na musamman a Garin Lokoja, inda bayan taron a ka tsaida matsayar cewa ya kamata a biya Malaman Kogi kudinsu.

BESAN ta ce silar rashin biyan Malaman albashinsu shi ne wani aiki da gwamnatin jihar Kogi ta dauko na bin diddikin ma’aikatan ilmi, inda wannan bincike ya sa Malamai su ka koma Maroka.

Wannan hali na rashin albashi a gwamnatin Yahaya Bello ta sa Malamai da yawa sun buge da shiga halin maula domin samun abin da za su ci. Malamai fiye da 23, 000 wannan ya shafa a jihar.

KU KARANTA: Wani Gwamna zai fara biyan sabon albashi kwanan nan

Shugaban kungiyar BESAN na jihar Kogi, Onotu Yahaya da kuma Sakatarensa Mohammed Sule ne su ka sa hannu a takardar matsayar da aka cin ma bayan taron da aka yi Ranar 23 ga Satumba.

BESAN ta kuma koka game da yadda gwamnatin Kogi ta gaza dabbaka tsarin N18, 000 a matsayin mafi karancin albashi wanda aka yi shekara kusan 8 da farawa a sauran jihohin da ke Najeriya.

Wannan kungiya ta ce haka zalika akwai tsofaffin Malaman makarantar da su ka yi ritaya tun tuni amma har yau babu labarin biyansu kudi sallama, sannan kuma ba a biyan su kudin fansho.

Yahaya ya yi kira ga hukuma ta daina biyan Malamai gutsure na kashi 35% ko 40% daga cikin albashinsu, sannan an nemi gwamnan na APC mai ikiarin canji da ya gyara makarantun jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel