Tirkashi Shekarau na tsaka mai wuya: Kotu za ta hana Shekarau, Aminu Wali da wasu mutane fita daga Najeriya

Tirkashi Shekarau na tsaka mai wuya: Kotu za ta hana Shekarau, Aminu Wali da wasu mutane fita daga Najeriya

- Wata babbar kotu dake zaune a Kano ta nemi tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau, Ambasada Aminu Wali da kuma Injiniya Ahmed Mansur fita daga Najeriya

- Kotun ta bayyana hakan ne bayan zargin su da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi akan fitar da miliyan 950 ta hanyar da bata dace ba

- Kotun ta bukaci Sanatan da mukarrabansa akan su bayar da takardunsu na fita kasar waje, domin a cigaba da bincike a kansu

Shekarau da Wali tsofaffin ministoci ne a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Mansur kuwa tsohon darakta janar ne na yakin neman zaben tsohon shugaban kasar a shekarar 2015.

Kotun wacce mai shari'a Lewis Ambrose Allagoa yake jagoranta ta zauna a jiya Litinin inda ta bayyana cewa hujjojin da wadanda ake zargin suka kawo ba su isa su sanya kotu tayi watsi da shari'arsu ba.

Kotun ta nemi mutane ukun da ake zargi da su bayar da takardunsu na fita kasashen waje, wanda aka ba su kwanan nan aka zuwa duba lafiyarsu.

KU KARANTA: Asiri ya tonu: Dan majalisa yayi min fyade, sannan yayi mini alkawarin bani miliyan 20 idan na takura mijina ya sake ni

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa dai ita ce ta kai wadannan mutanen kotu akan zarginsu da take yi da safarar kudade ta hanyar da bata dace ba, da kuma karya dokar yakin cin hanci da rashawa.

Hukumar ta zargi mutane ukun da karkatar da naira miliyan 950 daga jam'iyyar PDP, inda ta bayyana cewa kudaden wadanda aka karbe su hannu da hannu sun sabawa dokar yaki da cin hanci.

Haka kuma hukumar ta bayyana cewa Shekarau, da abokanan nasa guda biyu sun fitar da kudin ta hanyar da ba ta dace ba.

Yanzu haka dai kotu ta daga sauraron karar har zuwa ranar 18 ga watan Nuwambar wannan shekarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel