Najeriya ta samu fiye da Naira Tiriliyan 28 a shekaru 5 – NEITI

Najeriya ta samu fiye da Naira Tiriliyan 28 a shekaru 5 – NEITI

Hukumar “Nigeria Extractive Industries Transparency Initiative” wanda aka fi sani da NEITI ta bayyana cewa an zuba Naira Tiriliyan 28.58 a cikin asusun Najeriya a cikin shekaru kusan biyar.

Wannan hukuma mai bin diddikin yadda aka batar da kudi a kasar ta ke cewa daga shekarar 2012 zuwa 2016 ne Najeriya ta samu wannan makudan kudi daga man fetur, arzikin alatu da haraji.

NEITI ta bayyana wannan ne a lokacin da ta fitar da rahoton binciken da ta yi na shekarar 2012 zuwa 2016. An fitar da rahoton ne a babban birnin tarayya Abuja a Ranar Lahadin da ta wuce.

Babban Darektan yada labarai da wayar da kan jama’a na hukumar watau Dr. Orji Ogbonnaya Orji, shi ne ya fitar da wannan dogon rahoto gaban Duniya a Ranar 22 ga Watan Satumba, 2019.

Rahoton nan NEITI ya yi la’akari da wasu jihohi 9 na kasar da kuma hukumomi 4 da wasu tulun kudi 5 na musaman na gwamnatin tarayya wadanda su ka hada da akawun din rarar main a ECA.

Wadannan jihohi su ne Ribas, Bayelsa, Akwa Ibom, Nasarawa, Delta, Ondo, Imo, Kano da kuma Gombe. Hukumomin da aka yi bincike a kai su ne NDDC, PTDF, ETF da kuma hukumar PPPRA.

Daga cikin wannan Tiriliyan 28.5 da kasar ta samu a wannan lokaci, fiye da Tiriliyan 18 sun fito ne daga arzikin kasa idan har aka cire kudin tallafi da haraji. Sauran kudin sun fito ne daga haraji.

KU KARANTA: Dangote da Tsohon Ministan Najeriya sun samu matsayi a Duniya

Gwamnatin kasar ta samu fiye da Tiriliyan 3.73 daga harajin kaya na VAT, yayin da kashi 23% na abin da ya shiga cikin asusun kasar ya fito daga wasu hanyoyi daban da ba su da alaka da fetur.

A 2012 Najeriya ta samu Tiriliyan 4.19, sai Tiriliyan 4.73 a 2012, Tiriliyan 4.69 a 2014. A 2015 da 2016 abin da ya shiga cikin susun kasar shi ne Tiriliyan 2.89 da kuma Tiriliyan 1.65 inji hukumar.

Daga cikin kason man fetur da aka samu na Naira Tiriliyan 18.12, gwamnatin tarayya ta dauki Tiriliyan 8.32, jihohi kuma sun raba Tiriliyan 4.22. Kananan hukumomi sun tashi da Tiriliyan 3.25.

Wannan ban da Naira Tiriliyan 2.36 da aka warewa jihohin da ake hako wannan man fetur. A sauran kason kudin ban da kudin haraji na VAT, gwamnatin tarayya ce samun kashi mafi tsoka.

A duk wannan kaso da aka yi, Akwa Ibom ce ta fi kowace jiha cikin jihohin da aka yi bincike a kan su samun kudi. Delta ce ta zo ta biyu. Nasarawa da Gombe kuma su ne ke rukunin karshe.

Ribas da Bayelsa su ne su ka fi kowane dogara daga abin da ake samu daga man fetur. Da zarar babu kudin mai, jihohin za su fi kowa shiga matsala. Sai dai duk da haka ana kukan rashin kudi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel