Kotu ta yi ‘waje road’ da dan majalisan APC dake amfani da takardun karatu na bogi

Kotu ta yi ‘waje road’ da dan majalisan APC dake amfani da takardun karatu na bogi

Kotun sauraron korafe korafe na zabukan yan majalisu dake zamanta a garin Yolan jahar Adamawa ta yi awon gaba da kujerar wani dan majalisa daga jam’iyyar APC dake wakiltar mazabar Mubi ta kudu a majalisar dokokin jahar, Musa Bororo.

Rahoton jaridar Sahara Reporters ta bayyana cewa kotun ta yi waje road da Bororo ne sakamakon kama shi da laifin amfani da takardun karatu na bogi, biyo bayan samun sabani a sunayen dake jikin takardun karatun da yake ikirarin ya yi.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da yar bautan kasa a Jos

Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun, Mai Sharia Akanbi ya bayyana cewa Bororo ya mika ma hukumar zabe mai zaman kanta, INEC takardun shaidar kammala karatu dake dauke da sunaye daban daban.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito akwai takardun dake dauke da sunan Musa Umar, yayin da wasu kuma ke dauke da sunan Musa Bororo, wanda hakan tasa Alkalan kotun suka ce wannan ya nun aba takardunsa bane.

Daga karshe Mai Sharia Akanbi ya sutale Musa Bororo daga kan kujerar dan majalisa mai wakiltar mazabar Mubi ta kudu, inda ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta baiwa dan takarar jam’iyyar PDP, Yakubu Dirbishi takardar nasara a matsayinsa na halastaccen zababben dan majalisa.

Sai dai da yake tsokaci game da hukuncin, Bororo yace bai gamsu da hukuncin kotun ba, don haka zai daukaka kara zuwa kotun daukaka kara don kwatar hakkinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel