Kotun zabe ta sauke mataimakin kakakin majalisar jiha, karkashin jam'iyyar PDP

Kotun zabe ta sauke mataimakin kakakin majalisar jiha, karkashin jam'iyyar PDP

- Kotun sauraron kararrakin zabe da ke Makurdi a jiha Benue, ta sauke kakakin majalisar jihar

- Mai shari'a Odudu ya yi hakan ne sakamakon ganowa da ya yi cewa tazarar kuri'un da suka kai Adaji ga nasara basu kai yawan kuri'un da aka soke ba

- Adaji ya ce hakan ba barazana bace ga kujerarsa don kuwa zai daukaka kara

Kotun sauraron kararrakin zaben majalisar jihar Benue da ke Makurdi, ta soke zaben mataimakin kakakin majalisar jihar, Chris Adaji a ranar Litinin.

An bayyana Adaji a wanda ya lashe zaben kujerar majalisar jihar na yankin Ohimini na jihar Benue karkashin jam'iyyar PDP.

Amma kuma shugaban karar, Mai shari'a R. O. Odudu ya yanke hukuncin cewa yawan kuri'un da suka baiwa Adaji damar lallasa Musa Alechenu Ohimini na jam'iyyar APC basu kai yawan kuri'un da aka soke ba. Hakan kuwa yaci karo da dokar zaben.

A zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta yanke hukunci, Adaji ya lashe zaben ne da banbancin kuri'un 397.

Amma kuma sai kotun ta gano cewa, kuri'un da aka soke sun kai 1,056 daga akwatuna biyu na Igbanomaje da Odega.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta sallama tsohon sanatanta da ya koma jam'iyyar

Mai shari'a Odudu ya ce bai kamata hukumar zaben mai zaman kanta ta yanke hukunci ba, ba tare da ta sa an kara zabe a akwatunan da aka soke.

Amma Adaji ya ce, zai daukaka kara saboda hukuncin kotun bai gamsar da shi ba.

Adaji ya yi bayanin cewa matsayinsa na mataimakin kakakin majalisar jihar bai tabu ba da hukuncin.

Adaji ya ce, "Yankunan biyu da ake magana akai duk yankunan da nake da rinjaye ne. Ko sau nawa za a yi zabe kuwa zan lashe."

"Zan tattauna da lauyoyina don sanin me yakamata in yi yadda zamu hadu a kotun daukaka kara," in ji mataimakin kakakin majalisar jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel