Messi ya sake kafa tarihi a duniyar kwallon kafa, ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya

Messi ya sake kafa tarihi a duniyar kwallon kafa, ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya

Dan wasan gaba a kasar Argentina da kungiyar Barcelona, Lionel Messi, ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan kafa na FIFA na wannan shekarar, wanda aka yi bikin bayar wa a Milan, kasar Italy.

Messi ya kayar da sauran abokan takararsa; Cristiano Ronaldo na kungiyar Juventus da Virgil van Dijk na kungiyar Liverpool, wadanda aka zaba a matsayin masu takarar neman kyautar.

Ronaldo da Van Dijk sun lashe manyan kyautuka.

Wannan shine karo na shidda da aka zabi Messi a matsayin wanda ya lashe kayautar gwarzon dan wasan FIFA na shekara.

A sauran rukunin kyaututtukan da aka bayar, Jorgen Klopp na kungiyar Liverpool ya zama mai horarwa mafi kwarewa a kakar bana. Klopp ya kayar da sauran abokan takararsa; Peo Guardiola mai horar wa a kungiyar Manchester City da Mauricio Pochettino mai horar wa a kungiyar Tottenham.

DUBA WANNAN: Mahaifiyata ta tsine min saboda na koma addinin Musulunci - Matashiya

Mai tsaron ragar kungiyar Liverpool ya zama mafi kwarewa a kakar wasannin bana bayan ya doke abokan takararsa; Ederson, mai tsaron raga a ungiyar Manchester City da Mac-Andre ter Stegen, mai tsaron raga a kungiyar Barcelona.

An bawa kociyan kungiyar Leeds United, Marcelo Bielsa, kyautar hakuri da adalci bayan ya bukaci 'yan wasan kungiyarsa su bar kungiyar Aston Villa ta farke kwallon da suka zura a ragarsu yayin wani wasa da suka buga a watan Afrilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel