Kungiyar ISWAP tace ta kashe sojojin Najeriya 2

Kungiyar ISWAP tace ta kashe sojojin Najeriya 2

Kungiyar yan ta’adda reshen yammacin Afirka wacce aka fi sani da ISWAP ta fitar da wani bidiyo da ya nuna yadda mayakanta suka hallaka wasu mutune biyu da ta ce dakarun sojin Najeriya ne, shafin BBC ta ruwaito.

Kungiyar ta yi ikirarin cafke sojojin ne a farkon watan Satumba, lokacin da mayakanta suka kaddamar da hari a wani barikin soji a jihar Borno.

Faifai bidiyon da kungiyar ta fitar a ranar Lahadi na zuwa ne bayan da rundunar sojin kasar ta bayyana cewa dakarunta na samun nasara a yakin da take ke yi.

Rundunar ta ce sakamakon tsaurara hare-hare a kan 'yan kungiyar, mayakan na Boko Haram na tsere wa daga yankin tafkin Chadi zuwa yankunan Sudan da wasu kasashen Afirka.

A halin da ake ciki, dakarun Operation Lafiya Dole na rundunan sojin Najeriya a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Lahadi, 22 ga watan Satumba, tace ta soma gudanar da aikin tantance mutanne a yankin Arewa maso Gabas domin tantance yan Boko Haram da mayakan kungiyar ISWAP wadanda ke buya a wassu kauyukan Borno da jihar Yobe.

KU KARANTA KUMA: Babu wata matsala Dan kujerar shugaban kasa ta cigaba da zama a arewa a shekarar 2023 - Ango Abdullahi

Rundunan sojin ta bayyana cewa an bukaci mazauna da kuma al’umman yankin arewa maso gabas da su dunga kasance dauke da katin shaida mai inganci a jihohin Adamawa, Borno da Yobe.

Kakakin dakarun, Kanal Ado Isa, a wani jawabi da yayi a ranar Lahadi yace an umurci dakarun rundunar dasu gudanar da bincike da kuma duba ingantaccen katin shaidar al'umman yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel