Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da yar bautan kasa a Jos

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da yar bautan kasa a Jos

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun afka har cikin gidan wata budurwa dake aikin yi ma kasa hidima, watau NYSC, dake garin Jos na jahar Filato, inda suka yi awon gaba da ita da nufin yin garkuwa da ita.

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito yan bindigan sun yi garkuwa da yar bautan kasar mai suna Igwebuike Amilia Nkechi (mai lambar NYSC PL/19B/1423) ne da safiyar Litinin, 23 ga watan Satumbar shekarar 2019.

KU KARANTA: Shuwagabannin Arewa ne matsalar Arewa – Hakeem Baba Ahmad

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da yar bautan kasa a Jos
Nkechi
Asali: UGC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Nkechi tana aikin bautan kasa ne a sakatariyar karamar hukumar Jos ta Arewa a jahar Filato, kuma miyagun sun dauketa daga gida ne da misalin karfe 4:30 na dare a gidanta dake kusa da AA Garden, titin Rukuba.

Zuwa yanzu yan bindigan sun tuntubi iyayen Nkechi, kuma sun nemi a biyasu kudin fansa naira miliyan 5 kafin su sakota. Wata majiya daga hukumomin tsaro a jahar ta tabbatar da sace Nkechi, inda tace da misalin karfe 8:45 suka samu labari, kuma miyagun sun tuntubi yan uwanta a jahar Ribas da Delta don neman biyan kudin fansa.

Haka zalika kaakakin hukumar NYSC reshen jahar Filato, Jennifer Laha ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta kara da cewa sun kan hanyarsu zuwa babban ofishin Yansandan jahar Filato domin ganawa da kwamshinan Yansanda.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu tayi na jin ta bakin kaakakin Yansandan jahar Filato, DSP Tyopev Terna da shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa, Philiph Izang ya ci tura sakamakon dukkaninsu basu amsa wayarsu ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel