Kudin yakin neman zabe: Shekarau, Wali da Mansur sun shiga 'tsaka mai wuya'

Kudin yakin neman zabe: Shekarau, Wali da Mansur sun shiga 'tsaka mai wuya'

A ranar Litinin ne wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Kano ta umarci tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, da Bashir Aminu Wali; tsohon ministan harkokin kasashen ketare a mulkin tsohon shugaba Goodluck Jonathan, da Injiniya Ahmed Mansur; tsohon darektan yakin neman zaben Jonathan/Sambo a kano, da su shirya fara kan su a kan zarginsu da badakalar miliyan N950 da hukumar yaki da karya tattalin arziki (EFCC) ke yi.

Kotun da ke karkashin Jastis Lewis Amburus Allagoa ta ce ba zata kori tuhumar da ake yi wa mutanen uku ba kamar yadda suka nema, saboda ba ta gamsu cewa babu tuhumar da zasu amsa ba, kamar yadda suka bayyana a baya.

Bayan sauraron bayanai da hujjojin masu kara, Jastis Lewis ya ce kotun ta gamsu cewa akwai bukatar Sanata Shekarau da sauran mutanen biyu su wanke kansu a gaban kotun daga zargin da EFCC ke yi musu.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da mutanen uku a gaban kotun bisa zarginsu da laifukan da suka hada da almundahanar kudi da kuma saba dokokin yaki da cin hanci da rashawa na kasa.

EFCC ta zarge su da karbar miliyan N950 daga hannun jam'iyyar PDP a matsayin kudin yakin neman zabe a shekarar 2015, lamarin da hukumar EFCC ta ce ya saba wa tanadin doka.

DUBA WANNAN: Garkuwa da mutane da fashi da makami: Rundunar soji ta kori jami'anta uku

Kazalika, hukumar EFCC ta yi zargin cewa Shekarau tare da sauran mutanen biyu sun raba adadin kudin da suka karba ta hanyoyin da suka saba da dokokin Najeriya a kan safarar kudade.

Bayan sun musanta dukkan zargin da ake yi musu, Shekarau, Wali da Mansur sun roki kotun ta yi watsi da karar bisa dogaro da cewa babu tuhumar da zasu amsa.

Bayan kotun ta ki amincewa da bukatarsu, ta umarci su dawo da dukkan wasu takardu da zasu iya amfani da su domin fita kasashen ketare, wadanda a baya kotun ta basu bisa dalilai na neman lafiya.

Yanzu haka kotun ta daga sauraron karar zuwa ranakun 18 zuwa 19 ga watan Nuwamba domin wadanda aka gurfanar su fara kare kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel