Babu wata matsala Dan kujerar shugaban kasa ta cigaba da zama a arewa a shekarar 2023 - Ango Abdullahi

Babu wata matsala Dan kujerar shugaban kasa ta cigaba da zama a arewa a shekarar 2023 - Ango Abdullahi

Shugaban kungiyar dattawa arewa kuma tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello, Zaria, Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana cewa ba laifi bane idan mulki ta cgaba da kasance a yankin Arewa a shekarar 2023, idan har yan Najeriya suka yanke shawaran kada yawancin kuri’unsu ga yankin.

A cewar shi, kyakyawan nazari akan mukaman kabilu daban-daban ya nuna cewa anyi ma yankin Arewa fintinkau domin manyan mukaman kasar baya tare da ita.

Farfesa Ango har ila yau ya dage cewa babu laifi idan aka ba yankin mukaman shuwagabannin hukumomin tsaro kamar yanda sauran kabilu suka ji dadi kafin yanzu, ba tare da yankin Arewa tayi korafi ba.

"Abunda muke fuskanta a yanzu abun bakin ciki ne, muhawara masu hatsari aka sanya a gaba. mukamai nawa muke magana aka sannan sai kuce ana bangaranci a rabe-raben mukamai?

"Shin kun yi duba ga mukaman da ke ma'aikatun gwamnati da wadanda ke rike da su, toh menene na tayar da jijiyoyin wuya? Shin suna nuna son kai wajen aiwatar da ayyukansu game da sauran yankunan kasar?

KU KARANTA KUMA: Ya zama dole mazauna yankin arewa maso gabas su dunga daukar katin shaidar su, inji rundunar soji

"Wannan abun bakin ciki ne saboda hakan na tunzura mu zuwa fannonin da ba zai fisshe da kasar ba," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel